Nigeria Ban on Oil at the border
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Rufe iyakoki na iya kawo tashin hankali a Najeriya - Sada Soli

Sai ku latsa hoton da ke sama domin sauraron hirar da muka yi Sada Soli

'Yan Najeriya da dama ne musamman mazauna yankunan kusa kan iyakokin kasar da makwabtanta, ke ci gaba da mayar da martani game da matakin dakatar da kai man fetur zuwa gidajen man yankunan.

A ranar Alhamis Hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya ta ba da sanarwar dakatar da safarar man fetur zuwa gidajen man da ke kusa da kan iyakar kasar da zuwa nisan kilomita 20.

Hukumar ta ce ta dade tana zargi kan yawan gidajen man fetur d'in da ake bud'ewa a yankunan da ke daf da kan iyakoki, wadanda ga alama ana amfani da su ne wajen fasa-kwauri.

Kuma tun cikin watan Satumba ne, Najeriya ta tsuke kan iyakokinta da nufin dak'ile ayyukan fasa-kwauri musamman na shinkafa.

To, wannan mataki dai har ya fara jan hankalin wasu 'yan majalisar kasar da ke wakiltar al'ummomin irin wadannan yankuna.

Sada Soli, dan majalisa ne mai wakiltar mazabar tarayya ta Kaita da Jibiya, kuma a tattaunawar da yayi da BBC, dan majalisar ya ce matakin abin tayar da hankali ne don kuwa zai tsunduma jama'arsu cikin karin matsi.

Labarai masu alaka