Torreira ya gaji da cin benci a Arsenal, Inter na son sayen Giroud

Torreira bai samu damar buga wasa sosai ba a kakar bana Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan Arsenal Lucas Torreira zai tattauna da kociyan kungiyar Unai Emery bayan da ya fusata da yadda ake ajiye shi a benci tun bayan fara kakar wasar bana. (Mirror)

Inter Milan na sha'awar sayen dan wasan gaba na kungiyar Chelsea Olivier Giroud. (Gazzetta dello Sport - via Sun)

Mai horas da kungiyar Liverpool Jurgen Klopp ya tabbatar cewa babu yiwuwar kulob din ya sayi Kylian Mbappe duk da zakuwar da magoya baya suka yi bayan rade-radin cewa kungiyar za ta sayo dan wasan daga PSG. (Sun)

Madrid za ta bada Rodriguez ta karbi Pogba daga United da sauran labarai...

Real Madrid za ta bukaci a yi musayar yan wasa ita da Manchseter United, inda za ta bada dan wasan tsakiyarta James Rodriguez, domin karbar Paul Pogba. (El Desmarque, daga Metro)

Mai horar da yan wasan IngilaGareth Southgate ya ce ya kamata a tsaurara hukunci kan nuna wariya a kwallon kafa, bayan da aka hukunta kasar Bulgaria da tara tare da hana su buga wasa daya a filin kasar a dalilin nuna wariya ga wani magoyin bayan Ingila. (Express)

Mai tsaron bayan Man U Marcos Rojo ya tattauna da Everton kan yiwuwar kulla yarjejeniya da kulob din kafin fara kakar wasannin badi. (Manchester Evening News)

Tsohon mai horar da Arsenal Arsene Wenger ya ce abin da mai horar da 'yan wasan kulob din ya yi na amshe kambun kyaftin daga hannun Granite Xhaka daidai ne. (Evening Standard)

Labarai masu alaka