Halin da ake ciki a fagen wasannin kwallon kafa na Turai

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Arsenal ta fara tattaunawa da tsohon mai horar da Sfaniya da Barcelona Luis Enrique don duba yiwuwar maye gurbin Unai Emery. (El Confidencial, via Metro)

Tottenham ta shirya biyan fam miliyan 50 ga dan wasan gaba na kasar Holland Memphis Depay da ke wasa a Lyon. (Sunday Mirror)

Dan wasan ya taba buga tamaula a Manchester United. (Sunday Mirror)

Chelsea na bukatar fam miliyan biyar ga duk wani kulob da ke son sayen dan gabanta Olivier Giroud a watan Janairu. (Sunday Mirror)

Mai horar da 'yan wasan Liverpool Jurgen Klopp ba zai bar mai tsaron baya Dejan Lovren ya bar kulob din a watan Janairu ba. (Football Insider)

Juventus za ta ba da daya daga cikin 'yan wasanta Mario Mandzukic ko Emre Can ko Daniele Rugani, ko kuma Blaise Matuidi don yin musaya da Paul Pogba na Manchester United. (Sunday Express)

Tottenham da Man U da kuma PSG sun nuna sha'awar sayen mai tsaron ragar Kamaru da a yanzu ke wasa a Ajax, wato André Onana. (Sunday Mirror).

Hukumar da ke shirya gasar Zakarun Turai na duba yiwuwar gudanar da wasan karshe na gasar a Amurka. (Morning Consult)

Za'a iya buga wasan karshe na Zakarun Turan shekarar 2024 a birnin New York, wanda zai zama na farko da aka taba buga gasar a wajen Turai a tarihi. (Morning Consult)