An yi wa Zahra Buhari ca kan taron ganawa da ita a N10,000

Zahra Buhari Hakkin mallakar hoto Zahra Buhari Instagram

'Yar gidan Shugaban Najeriya, Zahra Buhari Indimi za ta shirya wani taron kara wa juna sani game da matsalar nan ta tsangwamar mutane (musamman mata) a shafukan intanet.

Kamar yadda ta sanar a shafinta na Instagram, Zahra za ta bayyana irin halin da ta samu kanta a hannun masu amfani da shafukan sada zumunta bisa irin tsangwama da tsokana da ba'a da ta sha.

Kazalika, bakin da ta gayyata su ma za su bayyana nasu yanayin.

Wannan lamari dai ya jawo wasu 'yan Najeriya sun yi ta yi wa Zahra shagube da ganin cewa abu ne da bai kamata ta yi ba a irin wannan yanayin.

Sai dai BBC ta yi kokarin jin ta bakin Zahra kan ko me za a yi da kudin amma har zuwa lokacin yin wannan labarin ba a same ta ba.

Amma a kasan sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram, Zahra ta ce kudin za su shiga Gidadauniyarta ta ZMB Homes ne.

"Ina da labarina da nake ta hankoron na bayar na kwarin gwiwar da na samu duk da tsangwama da na fuskanta a intanet, kuma na san kuna da shi," Zahra ta wallafa.

Ba kyauta za a shiga ba

Duk da cewa halartar zauren taron ba kyauta ba ne amma akwai rahusa ga mutum 15 na farko, inda za su biya N6,000 kacal.

Wadanda ba su yi sa'ar kasancewa cikin mutum 15 din farkon ba kuma to za su biya naira dubu 10 domin jin labari tare da tattauna wa da Zahra.

Kazalika kujerun kadan ne, saboda haka Zahra ta ce "a yi rijistar neman shiga ta hanyar imel" ba sai an je kafa da kafa ba.

"Ina zumudin na gan ku! Ku tabbata kun turo sakon imel din nan yanzu," Zahra ta ce.

Me ya jawo ce-ce-ku-cen?

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta da muhawara suna ta caccakar Zahra da cewa "wacce irin tattaunawa ce da har sai an biya kudi kafin a samu damar halarta?'

A ganin su ya ya za a yi 'yar shugaban kasa guda ta hada taron ganawa da ita kuma ta ce sai an biya kudin shiga?

Zahra dai ta ce kudin da ta tara daga taron za su shiga Gidauniyar ZMB Homes ne.

Ita wannan gidauniyar dai Zahra na amfani da ita ne wajen tallafa wa marayu da 'yan gudun hijira a sassan Najeriya daban-daban.

Ga wasu daga cikin abubuwan da aka wallafa a shafukan sada zumunta kan batun:

Labarai masu alaka