Me INEC ta je yi ofishin PDP?

Tattaunawarmu da Sanata Umaru Tsauri Hakkin mallakar hoto Others

Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi kira ga hukumar zabe da ta kirkiri dokar zabe da za ta bada damar jefa kuri'a ta amfani da kwamfuta.

Shugaban jam'iyyar Uche Secondus ne ya bayar da shawarar a lokacin da ya ke karbar tawagar hukumar zaben a yayin wata ziyara da ta kai zuwa sakatariyar jam'iyyar ta kasa da ke Abuja.

Kan wannan ziyara da kwamitin INEC ya kai sakatariyar PDP ne BBC ta tuntubi sakataren jam'iyyar na kasa, Sanata Umar Tsauri don jin karin yadda ziyarar ta kasance.

BBC: Me ya janyo aka yi wannan taro tsakanin hukumar zabe ta kasa da jam'iyyarku ta PDP?

Sanata Tsauri: To mun yi wani taro tare da hukumar zabe INEC kan wata bukata da suka bayyana a wata wasika da suka ruuto mana. Sun ce suna so su tantance wasu abubuwa daga bangaren jam'iyyar mu. Wannan bukata sun rubuto ta ne kimanin mako uku da ya gabata.

BBC: Kamar wadanne abubuwa suke son tantancewa?

Sanata Tsauri: Hukumar zabe ta so ta sani cewa ofishin da jam'iyyar PDP ta ke amfani da shi mallakin mu ne ko kuwa muna haya ne a cikinsa. Na biyu kuma sun je su duba yadda muke tafiyar da jam'iyya ta bangaren yadda muke samowa da kashe kudade kamar yadda tsarin mulkin kasa ya ba su dama.

Na uku kuma suna son sanin yadda muke adana sunayen 'ya'yan jam'iyyar PDP.

BBC: Kana nufin 'yan takara ke nan?

Sanata Tsauri: A'a. Ina nufin daukacin 'yan jam'iyyar PDP. To hukumar INEC ta ce tana bukatar ganin rajistarmu ta 'yan jam'iyyar mu ta PDP. To Alhamdu lillah, mafi yawan abubuwan da suka nema, sun zo kuma mun ba su.

Labarai masu alaka