Solskjaer ya ce Man Utd za ta iya korarsa, Pochettino zai dawo Firimiya

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mai horar da yan wasan Manchester United Ole Gunner Solskjaer ya fadawa yan wasan sa cewa za'a iya sallamarsa daga aiki la'akari da yadda wasannin da za su buga da Tottenham da kuma makwabtansu Manchester City. (Sun)

A wata mai kama da haka tsohon dan wasan gaban Man Utd Zlatan Ibrahimovich ba zai karbi kwantiragi daga wata kungiya a gasar firimiya ba.

Rahotanni sun ce Zlatan na shirin kulla yarjejeniya da tsohuwar kungiyar sa wato AC Milan na Italiya. (Telegraph)

Hakama an taya wa AC Milan din dan wasan gaban Chelsea Olivia Giroud. (Calciomercato)

Dan wasan tsakiyar Tottenham Christian Eriksen ya ce babu wani abu da zai sa ya karbi sabuwar yarjejeniya da kungiyar. (Telegraph)

Hukumar gudanarwar Arsenal na son a baiwa tsohon dan wasan kungiyar Mikel Arteta jan ragamar kungiyar, domin ya maye gurbin Unai Emery da a ka sallama. (Mirror)

A yanzu Arsenal na da jan aikin tantance masu neman horar da kungiyar da suka kai mutun 12. (Mirror)

To amma duk da haka Arsenal za ta iya ba Freddie Ljungberg mai shekaru 42 jan ragamar kungiyar, matsawar ya taka rawar a zo a gani a matsyain kocin rikon kwarya. (Evening Standard)

Tsohon mai horara da yan wasan Tottenham Mauricio Pochettino ya ce a shirye ya ke tsaf don dawowa fagen daga. (Fox Sports, via Mirror)

Roy Hodgson na Crystal Palace ya ce yana yana sa ran dan wasan gaban kungiyar Wilfred Zaha mai shekaru 27 zai tsaya da kungiyar da ke birnin Landan har shekarar 2023, lokacin da kwantiraginsa za ta kare. (Sky Sports)