Rashin tsaro: Kasashen Afirka ta Yamma sun tattauna

@

Asalin hoton, Getty Images

Shugabannin kasashen yammancin Afirka sun yi taro a Najeriya kan magance matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa a yankin.

Ana sa ran taron zai mayar da hankali musamman a kan karuwar ayyukan masu tayar da kayan baya a yankin Sahel.

A karshen taron ana sa ran shugabannin za su samar da mafitar da wani shiri kan yadda za su mangance matsalar tsaro a yankin nasu.

Karuwar hare-haren masu da'awar jihadi ya sa shugabannin yankin Afirka ta Yamma na fuskantar karin matsin lamba daga cikin gida da kasashen duniya.

Kimanin soja 200 ne da kuma fararen hula da dama mayakan masu ikirarin jihadi suka kashe a Nijar da Mali da Burkina Faso a cikin watanni ukun da suka gabata.

Taron shugabannin yankin na zuwa ne jim kadan bayan Amurka da Burtaniya sun soji kasashen yankin da gazawa wurin yin abin da ya dace domin kawo karshen ayyukan masu tsattsauran ra'ayin addini a yakin.

Amurka da Burtaniya sun bayyana cewa matakin soji kadai ba zai iya magance matsalar tsaro a yankin ba, amma shugabannin yankin na yawan yin kira ga kasashen duniya da su taimaka wajen kawo karshen matsalar.