Muna neman kotu ta halasta karuwanci karara - Karuwai

Asalin hoton, AFP
Wasu mata masu zaman kansu guda 16 sun shigar da karar neman kotu ta ayyana karara cewa sana'ar karuwanci ba haramtacciya ba ce a Najeriya.
A farkon makon nan ne matan suka yi nasara bayan wata kotu da ke zamanta a Abuja, ta yanke hukuncin cewa an tauye hakkin matan da aka tsare da zargin karuwanci.
Matan sun shigar da karar ne bayan hukumomin birnin sun tsare matan a lokacin wani samame a wasu wurare mata masu zaman kansu ke tsayawa a Abuja.
Lauya mai kare masu karar Babatunde Ademola Jacob ya ce, sun yi maraba da hukuncin kotun, amma suna neman kotu ta yanke hukunci da zai ayyana karara cewa babu wata dokar kasar da ta haramta sana'arsu.
Kama mata masu zaman kansu da kuma tsare su ba bakon abu ba ne a Najeriya.
A watan Mayun wannan shekarar ne hukumomi suka tsare mata fiye da 60 a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja da zargin aikata karuwanci.
Sai dai wasu daga cikin matan sun yi zargin jami'an gwamnati da ci zarafinsu da kuma karbar kudade a hannunsu.
A zaman kotun da ta saurari karar, ta ce an tauye hakkokin matan da jami'an gwamnati suka kama, abin da ya sa ake tunanin hukuncin kotun ya halasta sana'ar karuwanci.