Iraqi: Masu zanga-sun kai wa jam'iyyun siyasa hari

Masu zanga-zanga a Iraqi na kallon hayakin da ya turnike bayan taho mu gama tsakaninsu da jami'an tsaro da ke neman kora su a watan Nuwamba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanga a Iraqi na kallon hayakin da ya turnike bayan taho mu gama tsakaninsu da jami'an tsaro da ke neman kora su a watan Nuwamba

Masu zanga-zanga a Iraqi sun cinna wuta a kan gine-ginen da jam'iyyun siyasa da mabiya akidar Shi'a ke amfani da su.

Masu zanga-zangar a garin Nassariyya da ke Kundancin Iraqi sun fusata ne bayan kisan da aka yi wa wani mai fafutukar siyasa a yankin.

Gine-gine da masu boren suka kai wa hari a yankin sun hada da ofisoshin manyan bangarorin Shi'ar kasar, ciki har da hedikwatar jam'iyar Dawa da kuma kuniygar Badr.

Nassariyya na daga cikin biranen Iraqi da aka fi samun kazamar zanga-zangar kin jinin gwamnati kasar, wadda aka fara tun a watan Oktoba a yankin Kudancin kasar.

A watan Nuwamba ne jami'an tsaron kasar suka kashe masu zanga-zanga mutum 21 a rana guda, bayan wata arangama tsakanin bangarorin biyu.

Masu zanga-zanga a fadin Iraqi na kira da a tsaftace tsarin siyasar kasar wadda jam'yyun mabiya akidar Shi'a suka yi kakagida.

Sauran bukatunsu sun hada da neman gwamanti da dauke su aiki sannan a kawo karshen cin hanci da rashawa a cikin aikin gwamnati.