Dan sanda ya harbe abokin aikinsa a Abuja

@

Asalin hoton, Inpho

Wani sufeton dan sanda ya bude wa abokan aikinsa wuta a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Dan sandan ya harbe wani kofur har lahira sannan ya raunata wani mataimakin sufeto, wato DSP.

Rundunar 'yan sandan Abuja ta ce daga bisani sufeton wanda bata bayyana sunansa ba ya harbe kansa har lahira.

A sanarwar da ta fitar yau Lahadi, kakakin rundunar ASP Mariam Yusuf ta ce abin ya faru ne a ofishinta na yankin Dutsen Alhaji da ke a karamar hukumar Bwari.

Yayin mika ta'aziyya ga iyalan mamatan, kwamishinan rundunar Bala Ciroma, ya umurci a gudanar da bincike domin gano musabbabin lamarin da kuma daukar matakan kare sake aukuwar hakan.

Rundundar ta bukaci mazauna da su cigaba da gudanar da harkokinsu cikin lumana, sannan ta ba su tabbacin isasshen tsaro a lokacin bukukuwan karshen shekara.