Iraq: Masu zanga-zanga sun ba da sharadin nada shugaba

@

Asalin hoton, AFP

Dubun dubatar masu zanga-zanga a Kudancin Iraqi sun gindaya sharuddan nada sahon shugaban gwamnatin kasar.

A yau ne wa'adin nada sabon firai ministan Iraqi ke cika bayan masu bore sun tilasta wa Adel Abdel Mahdi sauka daga mukamin.

Masu zanga-zangar da suka mamaye tituna a Karbala da Najaf da kudancin kasar sun ce dole sabon shugaban ya zama mara alaka da 'yan siyasa.

Sannan kada ya zama daya daga cikin mutanen da suka ajiye mukaminsu sakamakon zanga-zangar.

Suna kuma neman a kafa hukumar zabe mai adalci kuma mara alaka da 'yan siyasa ko jam'iyyu.

Mutanen sun tare hanyoyin zuwa babban birnin kasar Baghdad a cigaba da nuna kin jinin gwamnati.

A watan Nuwamban jiya ne masu zanga-zangar suka tilasta wa firai minista Adel Abdel Mahdi sauka daga mukaminsa.

An fara yajin aiki a Basra da Diwaniyah yayin da masu zanga-zangar ke neman a yi garambawul a gwamnatin kasar.

Suna zargin gwamnatin da cin hanci da rashawa da kuma gazawa wurin sauke nauyin da ke kanta.