'Yancin addini: Martanin Najeriya ga Amurka

Ministan yada labaran Najeriya, Lai Mohammed

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ministan yada labaran Najeriya, Lai Mohammed

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da wani rahoton Amurka da ke zarfin gwamnatin kasar da tauye 'yancin jama'a na yin addinin da suka ga dama.Wannan shi ne karon farko da sunan Najeriya ya fito a rahoton na shekara-shekara kan kasashen da gwamnatocinsu ke take hakkin yin addini.

Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed ya kwatanta ratohon da hukumar kare 'yancin yin addini ta Amurka ke fitarwa a duk shekatar a matsayin abin da aka dade da yin watsi da shi.

A sanarwar da hadiminsa kan yada labarai Segun Adeyemi ya fitar, Lai Mohammed ya ce mutanen Najeriya na da cikakken 'yancin yin addininsu a kasar.

Ya zargin marasa kishi musamman daga cikin malaman addini da 'yan siyasa da suka nemi yin amfani da addini domin samun kuri'u a zaben da ya gabata da rudin Amurka.

Sanarwar ta yi mamakin yadda rahoton ta sakataren harakokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fitar, ya yi rashin sa'ar fadawa tarkon mutanen da ke iya jefa Najeriya a matsala saboda adawa ko son zuciya.

Ya ce okarin miyagun na sanya addini a rikicin manoma da makiyaya da sauran rigingimun marasa nasaba da addini ya sa rahoton ke ganin gwamnati ba ta yin abin da ya dace ba kan 'yancin yin addini a Najeriya.

Babu kanshin gaskiya a danganta rikicin kabilanci ko na masu sana'a da addini face neman goga wa kasar kashin kaji, a cewarsa.

Game da kungiyar Boko Haram kuma ministan ya ce kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ce da ta saba wa sauran addinai, duk da ikiriarinta na bin addinin Islama.

Abin farin ciki a cewarsa shi ne gwamantin kasar ta yi kokari wurin magance rikicin manoma da makiyaya ta hanyoyi iri-iri, kuma tana samun nasara a kan kungiyar Boko Haram.

Game da tsare Sheikh Ibrahim al-Zakzaky da rahoton ya yi magana a kai kuwa, Lai Mohammed ya ce maganar aikata babban laifi kuma tana gaban kotu.

Ya ce gwamnati na maraba da suka mai ma'ana amma ba za ta lamunci kokarin haddasa kiyayya tsakanin bangarorin addini a kasar ba.