An yi arangama kan Musulmin China a Hong Kong

'Yan sanda na neman kama wani daga cikin masu zanga-zanga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan sanda na neman kama wani daga cikin masu zanga-zanga

An yi dauki ba dadi tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar goyon bayan Musulmin China a birnin Hong Kong.

Daruruwan masu zanga-zanga a Hong Kong sun yi gangamin nuna goyon baya ga Musulmi 'yan kabilar Uighur da ake musgunawa a China.

Mutanen na zargin hukumomin China da tura dubban Musulmai 'yan kabilar Uighur zuwa wasu sansanonin da ta kira na sake ilmantarwa.

Masu zanga-zanga da suka ce suna goyon bayan Musulmin sun kuma nuna fargabar samun kansu a irin halin da Musulman Uighur ke ciki.

Sun ce suna neman kawo karshen abin da suka kwatanta da karfa-karfar da China ke yi a gabashin Turkestan da sauran yankuna.