Yadda mutanen gari suka kori Boko Haram a Borno

Sojoji sun fatattaki Boko Haram kafin su shiga garin Biu

Asalin hoton, Getty Images

Rahotanni daga Biu da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu mahara sun kai hari da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Bayanai sun ce maharan sun kai harin da yammacin Litinin dab da lokacin sallar magariba sai dai jama'ar gari da da jami'an tsaro sun kore su suka hana su shiga garin.

Wani mazaunin garin na Biu ya shaida wa BBC cewa sun ji irin luguden wutar da maharan suka yi kuma yana tunanin lamarin ya rutsa da mutane da dama da suka zo cikin garin domin cin kasuwa.

A cewar shi "wasu da dama ba su samu sun koma gida ba saboda gudun kada harin ya rutsa da su wanda aka kai a shingen binciken jami'an tsaro."

Ya kara da cewa bayan da suka ji yadda maharan suka bude wuta ne ya sa mutanen gari dake yankin suka kai wa jami'an tsaro dauki.

Ya ce farar hulan sun nufi gidajensu domin dauko makaman da suke ajiye don shirin ko-ta-kwana domin bayar da tasu gudummawar wajen fatattakar maharan.

"Basu shigo Biu ba, an dakile maharan tun kafin su karasa zuwa wajen binciken jami'an tsaro.

Ya bayyana cewa zai yi wahala a iya bayyana 'yan Boko Haram din da wannan hari ya rutsa da su, haka ma a bangaren sojoji.

Ya ce suna kyautata zaton an kashe da dama daga cikin 'yan Boko Haram din.

Kawo yanzu a cewarsa komi ya lafa sai dai babu wani bayani da ya fito daga bangaren jami'an tsaron na Najeriya musamman rundunar da ke yaki da Boko Haram.

Ko a ranar Lahadi ma, 'yan Boko Haram din sun kai makamancin harin a Damaturun jihar Yobe inda mazauna garin suka ce masu-tada-kayar bayan sun yi musayar wuta ne da jami'an tsaro.