Manyan abubuwan da suka faru a Kannywood a 2019

  • Badariyya Tijjani Kalarawi
  • Broadcast Journalist

Wannan shafi ya tsakuro kadan daga cikin abubuwan da suka faru a harkarfina-finan Hausa ta Kannywood a shekarar 2019.

An karrama Ali Nuhu a India

A watan Oktoba ne wasu dalibai 'yan Arewacin Najeriya da ke karatu a kasar Indiya da malamansu Indiyawa suka gayyaci tauraron fina-finan Kannywood Ali Nuhu bikin Ranar Al'adu kuma suka karrama shi a wajen taron.

Jarumin ya ce baya ga wadannan dalibai, wasu makarantu a kasar sun ba shi lambobin yabo, cikinsu akwai makarantar Dayananda Sagar School of Physiotherapy su ma sun ba shi lambar yabo kuma sun nuna jin dadinsu kan yadda daliban Najeriya ke mayar da hankali kan karatunsu.

Ali Nuhu ya ce ya yi matukar farin ciki da wannan karramawa da kuma yadda malaman wadannan makarantu ke da sha'awar al'adun Hausawa.

Asalin hoton, OTHERS

Sunusi Oscar ya je jarun

A watan Agusta kuma hukumar ta ce fina-finai ta jihar Kano ta kama mai bayar da umarni Sunusi Oscar, kan zargin aikata ba daidai ba.

Wannan kamu da aka yi wa Oscar ya tayar da kura a Kannywood, inda 'yan fim kamar Sani Danja, da Mustapha na Baraska, da sauran abokan aikinsa suka kaddamar da wani gangami a shafin instagram da ke kiran a saki Oscar.

Ranar 16 ga watan ne dai kuma aka sake shi.

Asalin hoton, OTHERS

An kama Naziru Sarkin waka

A wata Satumba ne aka kama fitaccen mawakin nan Naziru Ahmad, wanda shi ne sarkin wakar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

An tuhumi Naziru ne kan wasu wakoki da ya yi kusan shekaru hudu da suka gabata, wato wakar Gidan Sarauta da Sai Hakuri.

Daga baya a watan ne kuma aka sake shi.

Asalin hoton, OTHERS

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Adam A Zango ya bar Kannywood

A ranar 15 ga watan Agusta ne fitaccen dan fim din Hausar nan Adam A Zango ya fito karara ya bayyana ficewarsa daga masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood.

Zango ya bayyana cewa rashin adalci da kazafi da kage da bita-da-kullin da ake yi a harkar ne suka tilasta ma sa daukar matakin.

Sai dai ya ce a yanzu zai fara cin gashin kansa ne, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.

A watan Satumba kuma Adam Zango ya karyata wani 'malami' da ya yi ikirarin cewa jarumin yana neman mata 'yan kasa da shekara 20 da zummar tantance su domin ya sanya su a wani sabon fim dinsa.

Sannan a Oktoba kuma Adam Zango ya sanar cewa ya biya kudin karatun wasu dalibai na shekara uku, inda ya kashe fiye da naira miliyan 46.

Sai dai batun ya jawo ce-ce ku-ce inda mutane da dama suka yi ta karyata lamarin, yayin da wasu kuma suka gaskata tare da jinjina wa kokarinsa.

Ya sake wallafa wani sako a shafinsa na Instagram, inda ya bayyana cewa a yanzu ya samar da hanyar da zai rinka fitar da sabbin fina-finansa ta intanet, inda masu kallo za su je su siya kuma su kalla. Ba a dauki lokaci ba sai Adam A Zango ya sanar da yin hijra daga arewacin Najeriya zuwa birnin Legas domin 'tsira da lafiyarsa'.

A Disamba ne kuma dai Adam ya sanar da yin hijirarsa daga arewaci zuwa kudancin Najeriya "domin tsira da lafiyarsa."

Asalin hoton, OTHERS

Rahama Sadau ta bude gidan abinci

A watan Disamba 'yar fim din Kannywood da Nollywood Rahama Sadau, ta bude wani wajen tande-tande da lashe-lashe a jihar Kaduna mai suna Sadauz's Lounge.

Sai dai an yi mata ca a shafukan sada zumunta sakamakon wallafa wasu hotuna da ta yi "masu bayyana wasu surori na jikinta".

Amma Rahama ta yi ta mayar da martani kan zagin da aka yi ta yi mata a shafin Twitter.

Fati Washa ta zama tauraruwar fina-finan Hausa a Birtaniya

Asalin hoton, OTHERS

Fitacciyar 'yar fim din Hausa Fatima Abdullahi da ake kira Fati Washa ta ci kyautar gwarzuwar jaruman Hausa a wani kasaitaccen bikin fina-finan Afirka da aka gudanar a Birtaniya a watan Nuwamba.

An sanar da Washa ne a matsayin gwarzuwar jaruma a taron karrama 'yan fim da aka gudanar a birnin Landan.

Fati Washa ta ci kyautar ne saboda rawar da ta taka a fim din 'Sadauki,' kuma ta doke Aisha Aliyu Tsamiya a fim din da ta fito "Jamila" da kuma Halima Yusuf Atete da ta fito a "Uwar Gulma."

Hadiza Gabon ta roki gafarar Allah

Asalin hoton, OTHERS

A watan Nuwamba ne Hadiza Gabon ta roki gafarar Allah a shafinta na Twitter, bayan da aka yi musu ca ita da kawayenta Rahama Sadau da Fati Washa kan wallafa wani hoto da suka yi a shafukan sada zumunta.

Rahama Sadau ce ta wallafa hoton a Twitter inda ta yi masa take da "ma ki gani ya kau da idonsa".

Sun dauki hoton ne a birnin Landan, lokacin da suka raka jaruma Fati Washa karbar kambun tauraruwar taurari a harkar fina-finan Hausa.

Sun sha caccaka sakamakon sanya hoton inda aka dinga yi musu zargi iri-iri na zina da madigo, abin da ya tunzura Gabon mayar da "kakkausan martanin" ga wani Bala Boyi.

Ba a jima ba ta yi saurin janye martanin da ta maida wa Bala Boyi da cewa "Astaghfirul Laah kan martanin da na mayar marar kyau kan wata amsar rashin da'a da wani ya ba ni. Na goge sakon kuma na nemi gafarar Allah kan kokarin mayar da martani cikin fushi kan wani kuskuren da aka yi."

Wannan ''abin kunya'' ya rikide ya koma na yabo ga tauraruwa Hadiza, inda fitaccen malamin addinin Musulunci kuma ministan sadarwa a Najeriya Sheikh Isa Ali Pantami ya yaba da abin da ta yi.

Asalin hoton, OTHERS

Rikicin Hadiza Gabon da Amina Amal

A watan Afrilu ne aka wayi gari da sabon lamarin ce-ce-ku-ce a Kannywood, kan batun alakar jaruma Hadiza Gabon da Amina Amal, inda Gabon ke zargin Amal na yada cewa "suna madigo tare."

Wani sako da matashiya Amal ta wallafa ne ya fara tayar da kura, duk da cewa ba ta ambaci sunan Hadiza a sakon ba, amma ba a jima ba ta fara mayar da martani.

Abin dai ya karade shafukan sada zumunta da janyo zazzafar muhara, bayan bullar wani bidiyo da Hadizar ta dinga kwada wa Amal mari, sannan tana maganganu cikin harshen Fulatanci.

Bidiyon ya janyo ana batun maka Hadiza Gabon gaban shari'a dan bin kadin dalilinta ''na cin zarafin Amal'' kamar yadda aka gani a bidiyon.

Hajiya Binta kofar soro ta rasu

Asalin hoton, OTHERS

Rai bakon duniya, a 2019 an tabo 'yan fim da mutuwar abokiyar aikinsu Hajiya Binta Kofar Soro, wadda ta rasu ranar Asabar, 4 ga watan Mayu a garin Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa, kafin rasuwarta ta yi fama da gajeriyar rashin lafiya.

Kafin rasuwar tauraruwar, ta wallafa a shafinta na Instagram inda ta bukaci al'ummar Musulmi da su yafe mata duk wanda ta yi wa laifi da wanda ba ta yi masa ba.

Asalin hoton, OTHERS

An tuna da rasuwar Ahmed S Nuhu da Hawwa Ali Dodo

A ranar daya ga watan Junairu ne akai addu'o'in tunawa da shahararren jarumin fina-finan Hausa marigayi Ahmad S Nuhu bayan da ya cika shekara 12 da rasuwa.

Jarumin ya rasu ne ranar 1 watan Janairun shekarar 2007 sandiyyar hadarin mota a Najeriya.

Hakazalika, a ranar an rika tunawa da tauraruwar fina-finan Hausa Hauwa Ali Dodo wadda ta rasu a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2010.

Wasu daga cikin masu harkokin fim sun bayyana irin kusancin da ke tsakaninsu da kuma kyawawan halayensu.