Saliyo za ta kawo karshen kaciyar mata

Mata da 'yan mata da masu fafutuka a lokacin gangamin yaki da yi wa mata kaciya

Kasar Saliyo na daga cikin kasashen duniya da matsalar yi wa 'ya'ya mata kaciya ta fi kamari. Kiyasin Majalisar Dinkin Duniya ya nuna kashi 80 cikin 100 na mata da 'yan mata a kasar an yi musu kaciya, kuma wata kabila mai suna BONDO ita ce ta fi kowace wannan al'ada.

Kasashe 28 a nahiyar Afirka su na yin wannan al'ada, wannan shi ne rabin kasashen nahiyar baki daya. A kasar Saliyo mata hudu cikin biyar sun fuskanci wannan matsala wadda ke janyo mummunar illa ga lafiyar mata wasu lokutan ma har da mutuwa.

Yayin da wasu ke karfafa gwiwar yin kaciyar da suke cewa kebance dadaddun al'adun da suka gada iyaye da kakanni, masu fafutuka a arewacin kasar sun zage damtse don ganin an kawo karshenta.

A karon farko an samo wasu mata da 'yan mata na BONDO da ba a yi musu kaciya ba. Kuma masu fafutukar sun je wani kauye mai suna Mathaska inda a baya ya yi kaurin suna wajen yi wa mata kaciya.

Masu fafutukar sun yi nasarar shawo kan matan da suke yin kaciya wadanda ake kira Soweis, sun kuma mika musu kayan da suke amfani da su tare da shan alwashin ba za su kara komawa aikin ba.

A baya dai hukumomi sun sha cafke irin matan tare da kai su gidan kaso, daya daga cikinsu mai suna Agnes Kanu wadda matar da ta yi wa kaciya ta mutu, ta shaida wa BBC cewa ta tsani al'adar da a baya ta ke jin dadin yi, ba kuma ta fatan sake aikatawa.

Hukumomin Saliyo da masu fafutuka da suka hada karfi da karfe don magance matsalar, na fatan ganin an kawo karshen ta nan ba da jimawa ba.