China na yi wa masu fafutuka 'kanshin mutuwa'

Gwamnatin Chana na tsare da daya daga cikin mutun goma 'yan kabilar Uighur
Bayanan hoto,

Gwamnatin China na tsare da daya daga cikin mutun goma 'yan kabilar Uighur

Kungoyin kare hakkin dan adam a China sun ce 'yan sanda a kasar sun kame akalla lauyoyi biyar da masu rajin kare hakkin bil adama da dama.

Haka ma kungiyoyin sun sanar da cewa kawo yanzu ba a ga wasu da dama ba.

Sun yi amanna cewa yin hakan wani mataki ne da gwamnati ta bullo da shi domin murkushe masu suka.

Rahotanni sun ce tun kusan mako daya kenan gwamnatin China ta fara kamen.

Kwana biyu kenan bayan da ta bayyana cewa hukumomin kasar sun yanke wa shugaban wata Coci ta 'yan Protestant da ke ayyukanta a boye, hukuncin zaman gidan yari na shekara tara bisa zarginsa da bijire wa gwamnati.

China na shan suka a fadin duniya musamman kan zargin muzguna wa musulmi 'yan kabilar Uighur da ke yankin Xinjiang.

To sai dai gwamnatin China ta musanta zargin inda kuma take mayar da martani a wasu lokuta.

Ba a jima ba da kasar ta dakatar da kallon wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a daukacin kasar, bayan da dan wasanta Mesut Ozil ya soki China kan muzgunawar.

Bincike ya nuna cewa sama da 'yan kabilar Uighur miliyan daya ne China ke tsarewa a duk shekara da sunan gyara hali, duk da binciken 'kwa-'kwaf da BBC ta gudanar ya tabbatar da akasin hakan.

Tuni 'yan kasar sun fara nuna adawa da matakin na baya-bayan nan na tsare masu fafutuka.