Amurka za ta dauki mataki kan shan tabar laturoni

An dade ana kira ga hukumomi da su dauki karin matakan hana matasa zama masu jarabar shan tabar ta laturoni.
Bayanan hoto,

An dade ana kira ga hukumomi da su dauki karin matakan hana matasa zama masu jarabar shan tabar ta laturoni.

Gwamnatin Shugaba Trump na Amurka ta sanar da cewa za ta haramta amfani da wasu tarin ganyaye da ake amfani da su a tabar laturoni, wadanda ke da kanshi ko dandano.

Ganyayen sun hada da na 'ya'yan itace da na'ana domin rage yadda matasa ke rungumar dabi'ar shan tabar ta zamani.

An dade daman ana kira ga hukumomi da su dauki karin matakan hana matasa zama masu jarabar shan tabar ta laturoni.

Wakilin BBC ya ce, jami'an lafiya na Amurka sun kuma yi la'akari da irin rawar da tabar da laturoni ke iya takawa wajen taimaka wa wadanda suka dade suna shan taba ta ainahi wato sigari, barin shanta.

Mutane 55 ne suka mutu a Amurkar sakamakon wata cuta ta numfashi da ba a kai ga gane ta ba kawo yanzu, wadda kuma ak sa ran na da ala'ka da shan tabar ta laturoni.

Hukumar da ke kula da abinci da magani ta Amurka ta ce za ta sa'ido tare da daukar mataki ga duk kanfanin da ya bijire wa umarnin hukumomi kan wannan batu.

Haka ma ta ce za ta fara kai samame bayan cikar kwanaki 30 da aiwatar da wannan doka.

Bayan mutuwar mutane 55 kan wata cuta da ke da alaka da numfashin, sama da mutane 2,000 yanzu haka na kwance a asibiti.