Shugaban kasa zai yi tattakin kilomita 200 a cikin daji

Yoweri Museveni mai shekaru 75 na daga cikin shugabannin da suka dade a kan karagar mulki.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Yoweri Museveni mai shekaru 75 na daga cikin shugabannin da suka dade a kan karagar mulki.

Shugaba Yoweri Museveni na Uganda zai yi tattakin har na tsawon Kilomita kusan dari biyu domin tuna baya kan gwagwarmayar da ya yi a shekarar 1986.

Hakan ya biyo bayan wucewar mulkin tsoffin shugabannin Uganda Idi Amin da kuma Milton Obote.

Mr Museveni zai shafe kwanaki shida a cikin dajin da su ka sha gwagwarmaya a lokacin tare da dakarunsa.

To amma 'yan adawa na kallon tattakin na shugaban a matsayin wani salon kamfe, ganin cewa badi ne za a gudanar da babban zabe a Uganda.

A na sa ran Museveni zai nemi wa'adi na shida.

Haka ma shugaban na fuskantar kalubale daga tsohon mawakin nan Bobi Wine, wanda ya bayyana kansa a matsayin jagoran talakawa.

Bayanan hoto,

Jagoran adawa Bobi Wine a baya ya sha dauri daga hukumomin tsaro a Uganda

Mr Museveni zai kammala tattakin ne a garin Birembo da ke yammacin kasar, wurin da a kayi kazamin fada tsakanin dakarun Mr Museveni da kuma shugaba mai ci a lokacin wato Milton Obote.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A cewar mai magana da yawun shugaban Don Wanyama yayin hira da kamfanin dillancin labarai na AFP, wannan tattaki tuna baya ne kan sadaukarwar da shugaban tare da sauran masu fafutuka suka yi don tseratar da al'ummar Uganda.

Yoweri Museveni mai shekaru 75 na daga cikin shugabannin da suka dade a kan karagar mulki.

A bana ne zai cika shekara 34 yana mulkin Uganda, bayan ya yiwa tsoffin shugabannin kasar Idi Amin da kuma Milton Obote juyin mulki.

Sai dai a martanin da ya mayar kan wannan tattaki, jagoran adawa Bobi Wine ya fadawa AFP cewa shugaban wahalar banza ya ke yi.

A cewarsa a maimakon kudin talakawa da zai kashe yana wannan tattaki,kamata yayi ya zauna ya yi nazarin wani abu daban, ya kuma gane cewa lokacin saukarsa mulki ya yi.

Jagoran adawar Bobi Wine a baya ya sha dauri daga hukumomin tsaro a kasar.

Shima wani jigo a jam'iyyar adawa Asuman Basalirwa ya ce wannan wani salon kamfe ne kawai, kuma ya kamata Mr Museveni ya fara shirye shiryen mika mulki a maimakon wannan tattaki da baya da wani anfani.