Venezuela: An hana Guaido shiga majalisa

Mista Guaido a lokacin da ya ke kokarin haura katangar majalisa tare da magoya bayansa

Sabuwar rikita-rikitar siyasa ta sake barkewa a kasar Venezuela, a daidai lokacin da aka haramtawa jagoran 'yan adawa Juan Guaido shiga majalisar dokokin kasar dan zabensa a karo na biyu.

Abokin hamayyarsa Luis Parra ya ayyana kan sa a matsayin shugaban majalisar, abin da magoya bayan Guiado suka kira kokarin juyin mulki a majalisa.

Tun lokacin da ya sauka daga mota tare da tunkarar babbar kofar shiga majalisar kasar, jami'an tsaro suka dakatar da Huan Guaido wanda ke sanye cikin bakar kwat da nekitayar mai launin Ja.

Ya yi kokarin shaida musu abin da suke yi ya sabawa doka amma ba su saurare shi ba, hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta sun ga yadda Mist Guaido da sauran magoya bayansa sukai kokarin haura katangar majalisar dan shiga ta karfin tuwo.

Amma hakan ta gagara, Mista Guaido ya ce a kan idonsu aka bar sauran 'yan siyasa na jam'iyyar adawa ta shugaba Nicolas Maduro da wadanda baya ga maciji da u da wadanda ke sukar lamirinsa suka shiga majalisar.

Gabannin wannan danbarwa, kamfanin dillancin labarai na AFP ya Ambato wani abokin hamayyar Mista Guaido Jose Brito na cewa, Mista Parra ne zai tsaya a matsayin shugaban majalisa, tare da cewa a yanzu ya zama tarihi.

Tuni kafafen yada labaran kasar na Radio da Talabijin suka sanar da Parra a matdsayin sabon shugaban majalisa tare da cikakken goyon bayan shugaba Maduro.

Venezuela ta fada rikita-rikitar siyasa a 'yan shekarun nan, ga kuma matsin tattalin arziki da ya dabaibaye kasar.

Sama da shekara guda kenan da jagoran 'yan adawa Juan Guaido ya ayyana kan sa a matsayin shugaban riko a Venezuela, inda sukai ta musayar yawu da zanga-zanga tsakanin magoya bayansa da na shugaba Nicolas Maduro.

Ofishin jakadancin Amurka a Venezuela, wanda ke birnin Bagota na kasar Colombia tun bayan rashin jituwa tsakanin kasashen biyu a shekarar da ta wuce, ya fitar da sanarwa tare da cewa haramtawa Mista Guaido shiga majalisar sam bai dace ba, sannan bas hi ne Muradin 'yan kasar ba.

Wani babban jami'in gwamnatin Amurka yace har yanzu kasarsa na kallon Mista Guaido a matsayin halataccen jagora, duk da cewa an zabi Lius Parra a matsayin shugaban majalisa.