Lafiya Zinariya: Hanyoyin samun haihuwa a likitance

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Dr. Mairo Mandara tare da Habiba Adamu

Ku latsa alamar lasifika domin sauraron Dr Mairo Mandara

Akwai hanyoyi da dama da kwararrun likitoci ke bi wajen taimaka wa ma'auratan da ba sa haihuwa su samu 'ya'ya.

A kasashen da suka ci gaba saboda ci gaban da aka samu a fannin kimiyya da fasaha mata da mazan da ke fuskantar matsalar rashin haihuwa kan je manyan asibitoci ko asibitoci na musamman, inda ake taikama musu ta hanyoyi daban-daban kuma a kan yi dace su samu rabo.

Sai dai lamarin ba haka yake ba a wasu kasashen da ke nahiyar Afrika da kuma wasu kasashen masu tasowa a wasu bangarorin duniya.

Akan samu karancin irin wadannan cibiyoyin lafiyar da ma kwararrun likitocin da za su yi aikin a irin wadannan kasashe.

Haka zalika a kasashe kamar Najeriya, ko da yake ana samun kwarrarun da ke bin hanyoyi na zamani wajen taimaka wa mata marasa haihuwa don samun juna biyu, amma akasari ba kowa ne ke iya biyan makudan kudaden da asibitoci masu zaman kansu ke cewa a biya ba.

A karashen tattaunawar da Habiba Adamu ta yi da Dr. Mairo Mandara kan batun rashin haihuwa, likitar ta yi mata karin bayani kan hanyoyin da mata za su iya bi domin samun haihuwa a likitance.

Labarai masu alaka