Saura kiris Amurka ta sake kashe wani kwamandan Iran

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Hukumomi a Amurka sun sanar da cewa sunyi yunkurin kashe wani babban kwamandan Iran a wani samamen sirri da suka kai a Yemen makon da ya gabata.

An shirya kisan Abdul Reza Shanlai wani babban kwamandan sojojin juyin juya halin Iran rana daya da kitsa kisan Janar Qassem Soleimani da Amurka ta kashe a Iraki makon jiya.

Yayin da a ka samu nasarar kashe Janar Soleimani, shirin kisan Abdul Reza bai yi nasara ba.

A baya Amurka ta zargi Abdul Reza Shanlai da daukar nauyin yakin da 'yan tawayen Houthi ke yi a Yemen.

Bugu da kari ta ce shi ke da alhakin kai harin da ya kashe sojojin Amurkar biyar a Iraqi a shekarar 2007.

Ko a watan Disamban da ya gabata ma'aikatar tsaron kasar ta ware tukuicin dala miliyan 15 ga duk wanda zai iya ba ta bayanan sirri kan inda Abdul Reza ke samun kudadensa da kuma su waye abokan huldarsa.

Har yanzu Shugaba Trump na ci gaba da kare matakin kisan Janar Soleimani.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Har yanzu Shugaba Trump na ci gaba da kare matakin kisan Janar Soleimani.

Ko a ranar Juma'a ya bayyana cewa Janar din na gab da kaddamar da hare hare kan ofisoshin jekadancin Amurka uku da ke gabas ta tsakiya kafin kisan nasa.

Ganin irin yadda Amurkar ta fusata Iran da kisan Janar Soleimani, masana na ganin yunkuri kisan Abdul Reza Shanlai zai 'kara tada zaune tsaye.