Rashin tsaro: Mutum '6000' na gudun hijira a Kaduna
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Rashin tsaro: Mutum '6000' na gudun hijira a Kaduna

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren rahoton Abdulsalam Ibrahim Ahmed kan rashin tsaro a Kaduna

Dubban mutane na tserewa daga kauyuka daban-daban na yankunan kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari inda suke neman mafaka a garin Buruku na jihar Kaduna a arewacin Najeriya.

Yankin dai na Birnin Gwari ya jima yana fama da rikice-rikice musamman na barayin shanu da 'yan bindiga dadi da kuma masu garkuwa da mutane.

A hare-haren da 'yan bindiga ke kai musu a 'yan kwanakin nan, al'amarin ya yi sandin asarar rayuka da raunata mutane da dama, baya ga awon gaba da ake zargin maharan sun yi da mutane da kayayyaki.

A tattaunawar BBC da wani mutumin yankin wanda bai so a ambaci sunansa, ya shaida cewa kauyukan da wannan lamarin ya shafa sun hada da Rimana da Malmo da Ba'da da Zankoro da Ba-dole da Ba-dumi da kuma Sarari.

A yanzu haka dai da dama daga cikin 'yan kauyukan suna garin Buruku na karamar hukumar Chukun ta jihar Kaduna, inda suka samu mafaka.

Wani daga cikin masu gudun hijirar ya shaida cewa akalla za su kai su 6,000 a garin na Buruku.

Masu gudun hijirar dai sun kunshi maza da mata da yara kanana.

Sun kuma shaida cewa ba su samu taimako daga wurin hukumomi ba ta fuskokin abinci ko magunguna ko kuma muhalli.

A nata bangaren, gwamnatin jihar Kaduna ta mayar da martani kan wannan lamarin inda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar Samuel Aruwan ya bayyana cewa gwamnatin jihar na da labarin abubuwan da ke faruwa kuma tana kokarin shawo kansu.

Matsalolin tsaro musamman na 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane na kara kazanta a jihohin arewa maso yammacin kasar musamman Katsina da Kaduna da jihar Zamfara.

Inda kuma yankin arewa maso gabashin kasar musamman jihar Borno 'yan kungiyar Boko Haram da Kuma ISWAP ne ke cin karensu ba babbaka.

Kadan daga cikin hare haren da aka kai a wannan makon

  • An sace wasu dalibai hudu na Kwalejin addinin Kirista ta Good Shepherd Major Seminary School da ke garin Kakau da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
  • 'Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu jami'an kwastam guda biyu a wani shinge da ke kauyen Dan-bedi a yankin karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina mai iyaka da Jamhuriyar Nijar.
  • Masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da fasinjoji kimanin 30 a karamar hukumar Batsari a jihar ta Katsina.
  • 'Yan bindiga sun kashe wani malamin jami'a a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
  • Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da matar dan majalisa mai wakiltar Miga a jihar Jigawa Haruna Aliyu a gidansa da ke jihar.
  • 'Yan bindiga sun lalata akalla gidaje 750 a garin Monguno da kashe sojoji uku.

Labarai masu alaka