Ana fargabar fashewar dutse mai aman wuta a Philippines

Hukumomi sun yi damara, an kuma shirya raba kayan agaji ga al'ummar da aka kwashe

Asalin hoton, Phivolcs

Bayanan hoto,

Hukumomi sun yi damara, an kuma shirya raba kayan agaji ga al'ummar da aka kwashe

Hukumomi a Philippines sun ba da sanarwar cewa akwai yiwuwar dutsen Taal da yanzu haka ke fitar da bakin hayaki babu makawa zai fashe.

Kusan babu wani abu da ke cin kasuwa a kudancin Manila a halin yanzu kamar hular rufe fuska, yayin da mazauna yankin ke tsammanin fashewar dutsen kowane lokaci daga yanzu.

Sai dai duk da dimbin bukatar wannan hula da ke rufe baki da hanci don gudun shakar gurbatacciyar iskar, hukumomi sun gargadi ma su shaguna da ka da su kara mata kudi.

To amma da yawa na ganin yakamata hankali ya karkata wurin ganin an yi shirin ko ta kwana don tunkarar matsalar a lokacin da dutsen ya fashe.

Kafin a je ko'ina akalla al'ummar da ke zaune a yankin na kudancin manila 15,000 ne aka kwashe, bayan ganin yadda hayakin Taal ya turnuke muhalli, yayin da ake tunanin zai iya fashewa nan ba da jimawa ba.

Hukumomi dai na fargabar afkuwar ibtila'in da ya faru a shekarar 1965, a lokacin da wani dutsen ya fashe ya kuma yi mummunar barna a yankin.

Yanzu dai bayan kwashe jama'a an kuma rufe hanyoyin da ke zuwa yankin da makarantu da ofisoshi, hadi da soke sauka da kuma tashin jirage a tashar jirgin kasa da kasa da ke babban birnin Philippens wato Manila.

Hakama hukumomi sunyi damara, yayin da aka shirya raba kayan agaji ga al'ummar da aka kwashe.