General Babangida on Biafra
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Biafra: IBB ya ce yakin basasar Najeriya ya hada kan 'yan kasar

Latsa hoton da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar

Tsohon Shugaban Mulkin Sojan Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce babban darasin yakin basasar kasar shi ne yadda al'ummar Najeriya suka yi saurin hade kansu sabanin kasashen da suka fuskanci irin yakin.

Janar Babangida ya bayyana wa BBC hakan ne lokacin wata hira ta musamman yayin da Najeriya ke cika shekara 50 da kawo karshen yakin Biyafara.

IBB kamar yadda wasu suke kiran shi ya ce a matsayinsa na daya daga cikin dakarun da suka yi yakin Biyafara kuma ya san irin abubuwan da suka faru.

"Mun san cewa abin da ya fi alheri ga kasar nan ta mu shi ne ya zamana muna kasa daya saboda hakan zai fi wa kowa alheri, da mutanen kudu da mutanen arewa."

A cewarsa, yawancin wadanda suke fafutukar ganin an raba Najeriya kamar kungiyoyin IPOB da MASSOB "yawanci ba su kai shekara 50 ba, ba su san abin da ya faru ba a da."

Yana mai cewa idan aka yi la'akari da abin da ya faru a lokacin yakin, mutane da yawa sun rasa ransu, wasu kuma sun samu nakasa.

Ya kara da cewa musabbabin yin yakin shi ne don a mayar da Najeriya "daya".

Game da masu neman a samar da tsarin karba-karba kuwa, tsohon janar din ya ce "Najeriya tana bin tsarin dimokradiyya ne."

"Kuma a tsarin ana barin kowa ya fadi ra'ayinsa, ya aikata abin da yake so cikin lumana da doka, kuma zancen karba-karba bai taso ba," a cewarsa.

Labarai masu alaka