Abin da ya sa muka yi yakin Biyafara – Yakubu Gowon
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Abin da ya sa muka yi yakin Biyafara – Yakubu Gowon

Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakkiyarhirar

Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya Janar Yakubu Gowon, wanda a karkashinsa ne aka fafata yakin Biyafara, ya ce sun shiga yakin ne "saboda kaunar Najeriya".

Gowon ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da BBC yayin da ake cika shekara 50 da kawo karshen yakin a ranar Laraba.

"Wannan yaki an yi shi ne saboda zaman Najeriya kasa daya, ba kamar yadda wasu suke son ballewa ba," in ji Gowon.

Ya ci gaba da cewa: "Saboda haka babu abin da zai sa na yi nadamar abin da muka yi domin kuwa kaunar Najeriya ce ta sa muka yi."

A cewarsa, an kammala yakin "ba wanda ya ci nasara kuma ba wanda ya kasa."

Tsohon shugaban kasar ya kuma bayyana ra'ayinsa kan masu neman a koma mulkin karba-karba inda ya ce "idan za a iya yin wannan kuma zai kawo zaman lafiya, a yi shi idan ana so."

Ya kara da cewa akwai lokacin da jam'iyyar PDP ta fara magana kan batun kuma "idan da an ci gaba da wannan watakila kabilar Igbo za su iya daukan mulki a lokacin, toh amma wannan bai yiwu ba."

Ya bayyana rashin damuwarsa kan aiwatar da tsarin na karba-karba "idan za a yi wannan a yanzu" yana mai cewa "kowa ne zai iya mulkin Najeriya."

"A Najeriya akwai mutane da yawa wadanda idan Ubangiji ya ba su wannan lokaci, idan za su iya yi don tsoron Allah, don kaunar jama'a, Najeriya za ta iya ci gaba yadda ya kamata."

A karshe tsohon shugaban ya gode wa Allah kan kawo karshen yakin shekara 50 da suka gabata.

Labarai masu alaka