Kamaru: Dalibi ya datse wa wani dalibi yatsa da adda

A Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani dalibi ya datse yatsar wani dalibi mai suna Anaud Alexandre Mbappe da adda a birnin Obala mai tazarar kilomita 50 a kudu da birnin Yaounde.

Al'amarin ya faru ne a wata makarantar gwamnati da ke wajen birnin Yaounde.

Daliban sun kaure da fada ne abin da ya sa daya daga cikinsu ya dauko adda wajen guntule yatsan abokin karatunsa.

Tuni dalibin yake samun kulawar likitoci a asibitin Obala.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da ake tsaka da batun wani dalibi dan shekara 15 ya daba wa malaminsa wuka har ya yi sanadiyyar mutuwarsa a Nkolbisson Yaounde.

Labarai masu alaka