Hazard ne gwarzon dan kwallon Belgium

Eden Hazard Hakkin mallakar hoto Getty Images

An bayyana Eden Hazard a matsayin gwarzon dan wasan Belgium da ke taka leda a waje, in ji Jaridar Het Laatste Nie HLN.

Wannan ne karo na uku a jere da dan wasan Real Madrid ke lashe kyautar, bayan 2017 da kuma 2018.

Hazard ya hada maki 458 a jerin 'yan wasan da ya yi takara, inda 'yan jarida da fitattu a kwallon Belgium kan zaba.

Kevin De Bruyne ne ya yi na biyu da maki 348, sai Romelu Lukaku na biyu mai maki 248, yayin da mai tsaron raga Thibaut Courtois ya yi na 13 da maki 26.

A shekarar 2019, Hazard ya lashe Europo League a Chelsea, daga nan ya koma Real Madrid da taka leda.

Shi ne ya lashe kyautar fitatcen dan wasa a gasar ta Europa kuma shi ne zakakurin dan wasan tawagar Belgium a bara.

Labarai masu alaka