Gobara ta kashe mutum takwas a gidan gajiyayyu a Czech

.

Asalin hoton, Reuters

Wata gobara da ta tashi a wani gidan gajiyayyu a Jamhuriyyar Czech ta kashe akalla mutum takwas.

Mutum uku sun samu raunuka a gidan da ke yammacin garin Vejprty da ke kan iyaka da kasar Jamus.

Babu wani cikakken bayani dangane da abin da ya tayar da gobarar. Jami'ai a kasar sun bayyana cewa masu bayar da agaji daga kasar Jamus sun taimaka wa jami'an na Czech amma tsananin yanayin sanyi na kawo cikas ga yunkurin nasu.

Wannan it ce gobara mafi muni a Jamhuriyyar Czech tun shekarun 1990 kamar yadda jaridar Lidové Noviny ta ruwaito.

A shekarar 2000, wasu mutane marasa muhalli tara suka mutu a wata gobara a Prague babban birnin kasar.

Garin Vejprty dai na da nisan kilomita 100 daga birnin Prague.

Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana ta kasar ya bayyana cewa sun samu rahoton gobarar ne da misalin karfe 03:49 agogon GMT.

Ya bayyana cewa motocin daukar marasa lafiya bakwai har da biyu na Jamus suka kai agaji a yayin da lamarin ya faru.

Ya kuma ce a yanzu haka dai gobarar ta daina bazuwa amma baza a ce an shawo kanta gaba daya ba.