Moses zai je Inter, Arsenal za ta sayi Boateng

Victor Moses ya haskaka sosai a lokacin zamansa Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Victor Moses ya haskaka sosai a lokacin zamansa Chelsea

Bruno Fernandez ya fada wa Sporting Lisbon cewa ya matsu ya tafi Manchester United.

Ana sa ran dawowa da tattaunawa kan kulla yarjejeniya tsakanin kungiyoyin biyu.(Sky Sports).

Mai tsaron bayan PSG Layvin Kurzawa zai tafi Arsenal a lokacin da kwantiraginsa za ta kare da kungiyar a watan Yuni.(France Football - in French).

Haka ma Arsenal din za ta yi kokarin kulla yarjejniya da mai tsaron bayan Jamus dake wasa a Bayern Munich Jerome Boateng a matsayin aro, kafin ta taya Dayot Upamecano na Leipzig a kan fam miliyan 50.(Star).

Inter Milan na ci gaba da kokarin kawo dan wasan tsakiyar Tottenham Christian Eriksen cikin lokaci kafin wasan da za su buga a gasar Serie A da Cagliari.(Mail).

A wata mai kama da haka Inter Milan din na da sha'awar kawo dan wasan bayan Najeriya Victor Moses da a yanzu ke zaman aro a Fenerbahce na Turkiyya.(Mirror).

Can kuwa a Spaniya Atletico Madrid ta taya dan wasan gaban PSG Edinson Cavani a kan kudi fam miliyan takwas da rabi.(L'Equipe - in French).

Mai horar da 'yan wasan Inter Antonio Conte ya zargi kociyan Tottenham Jose Mourinho da canza masa kalamai.(Mirror).

Real Madrid za ta gabatar da Reinier Jesus da ta saya daga Flamengo na Brazil kan yuro miliyan 30 a ranar Litinin, bayan da ya cika shekaru 18.(AS).