Gambia ta sha alwashin kama Jammeh

Yahya Jammeh

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Jammeh ya mulki Gambiya na shekara 22, an kuma zarge shi da take hakkin jama'a da azabtar da 'yan kasar

Ministan shari'ar Gambiya, ya ce duk ranar da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya yi kasadar dawowa kasar za su cafke shi.

Aboubacarr Tambadou, ya shaida wa BBC cewa zai so ya zartar da hukunci ga Jammeh kan irin mulkin zaluncin da ya yi a kasar.

Yahya Jammeh dai ya bayyana aniyar komawa gida, yayin da magoya bayansa suka ce cafke shi zai kai ga zubar da jini a Gambiya.

Mista Tambadou ya zargi Jammeh da karya tattalin arzikin kasar, da ya janyo ta zama saniyar ware tsakanin sauran kasashe da yin makarkashiya ga ci gaban Gambiya.

''Barnar da Jammeh ya yi wa Gambiya, za a dade ba a gyara ta ba, a kalla sai an dauki gwamman shekaru kafin kasar nan ta koma daidai, in ji ministan shari'ar.

Tun a shekarar 2017 ne tsohon shugaban yake gudun hijira a Equatorial Guinea, bayan hambarar da gwamnatinsa.

A shekarar 2016 ne kasar ta fada rikita-rikitar siyasa, bayan Jammeh ya sha kaye a zaben da aka yi a watan Disamba, inda kasashe makwabta suka aike da dakaru tare da tirsasa masa ficewa daga Gambiya.

Kalaman ministan shari'ar na zuwa ne, kwanaki kadan bayan magoya bayan tsohon shugaban sun gudanar da zanga-zanga tare da bukatar tsohon shugaban ya koma gida cikin aminci.

Mista Aboubacarr Tambadou ya zargi magoya bayan Jammeh da shirya zanga-zangar bogi, saboda sun tabbatar ba zai taba komawa gida nan kusa ba.

Mista Yahya Jammeh ya mulki Gambiya na tsahon shekara 22, an kuma zarge shi da take hakkin bil'adam ciki har da kisan gilla, da azabtarwa da tsare 'yan adawa da gwamnatinsa.

Sabuwar gwamnatin Gambiya karkashin mulkin Shugaba Adama Barrow, ta kafa wata hukumar tsage gaskiya dan binciken zarge-zargen take hakkin dan adam da cin hanci da rashawa na tsohon gwamnati.

Sai dai Mista Jammeh ya ki bai wa hukumar hadin kai dan gudanar da aikinsu.