Wane ne Bala Muhammad Kauran Bauchi?

Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Asalin hoton, Bauchi State Government

A farkon makon nan ne Kotun Kolin Najeriya ta bayyana Bala Muhammad, a matsayin halastaccen gwamnan jihar Bauchi, bayan karar da Muhammad Abdullahi Abubakar ya shigar yana kalubalantar zaben da aka yi masa.

Alkalan kotun baki daya sun yi imanin cewa hujjujojin da aka gabatar mata don kalubalantar zaben ba su isa a ce ta dogara da su wajen karbe kujerar gwamnan ba.

Bayan wannan hukunci ne BBC ta yi nazari kan rayuwar Bala Muhammad da rawar da ya taka a siyasa da kuma sauran abubuwan da ba ku sani ba game da shi.

Asalin hoton, Bauchi State Government

Rayuwarsa

An haifi Bala Muhammad a ranar 5 ga watan Octoban 1958, a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi.

Ya fara karatunsa na Firamare a shekarar 1965 a wata makaranta da ke kauyen Duguri, inda ya kammala a shekarar 1971.

Daga nan ya tafi makarantar sakandire a shekarar 1972, inda ya kammala a shekarar 1976.

Ya halarci kwalejin kimiyyar zane-zane ta shiyyar arewa maso gabashin Najeriya daga shekarar 1977 zuwa 1979.

Daga nan kuma sai ya soma karatunsa na digirin farko a jami'ar garin Maiduguri da ke jihar Borno a shekarar 1979, ya kuma kare a 1982, inda ya karanci harshen Ingilishi.

Bala Muhammad, ya kuma halarci kwalejin horas da harkokin gudanarwa a inda ya samu horo na dan wani lokaci.

Asalin hoton, Bauchi State Government

Bayanan hoto,

Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Sarautun Gargajiya

Sanata Bala Muhammad na rike da sarautun gargajiya da suka hada da;

  • Kauran Bauchi
  • Dangaladiman Duguri
  • Agunachebe Umueje.

Aikinsa na gwamnati

Alhaji Bala Muhammad, tsohon dan-jarida ne, an shafe tsawon shekaru ana gungurawa da shi a harkar.

Tsohon edita ne da rusasshiyar jaridar 'The Mirage' a shekarar 1982 - 1983, sannan tsohon mai aika rahotanni ne ga kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN.

Ya yi aiki da tsohuwar jaridar The Democrat, 1983 - 1984, sannan ya yi aiki da ma'aikatar cikin gida ta Najeriya tsakanin shekarun 1984 - 1994.

Kauran Bauchi ya taba zama babban jami'in shigo da kayayyaki a ma'aikatar albarkatun kasa ta Najeriya tsakanin 1995 - 1997, kazalika ya taba zama mataimakin darakta a ma'aikatar wuta ta Najeriya tsakanin 1997 - 1999

A shekarar 2003 ne ya zama daraktan gudanarwa na hukumar sufurin jiragen ruwa ta Najeriya.

Daga bisani ne kuma ya yi ritaya daga aikin gwamnati a kashin kansa ya kuma tsunduma siyasa.

Asalin hoton, Bauchi State Government

Bayanan hoto,

Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Siyasarsa

A shekarar 2007 ya tsaya takarar a karkashin jam'iyyar ANPP a matsayin dan majlisar dattawa mai wakiltar Bauchi Ta Kudu har ma ya yi nasara daga shekarar 2007 zuwa 2010.

A lokacin da tsohon shugaban Najeriya Umaru Musa 'Yar aduwa yake cikin halin jinya a Saudiyya, jam'iyyar adawa ta ANPP ta yi ta matsa lamba cewa a mika wa mataimakinsa Goodluck Jonathan mulkin kasar kafin ya samu lafiya.

Sanata Bala Muhammad na daga gaba-gaba wajen ganin an cimma wannan kuduri, don har a gaban majalisar dattawa sai da ya gabatar da bukatar hakan.

Wannan ce ta sa bayan mutuwar shugaban kasa 'Yar aduwa, da Jonathan ya hau mulki sai ya bai wa Bala Kaura mukamin ministan babban birnin tarayya Abuja, lamarin da ya sa Sanatan sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP daga ANPP, kamar yadda Buba Galadima ya shaida wa BBC.

Ya rike mukamin ministan Abuja daga shekarar 2012 zuwa 2015.

An ruwaito cewa akwai kyakkyawar alaka tsakaninsa da Shugaba Jonathan.

Asalin hoton, Bauchi State Government House

Bayanan hoto,

Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

EFCC ta taba tsare shi

Tun bayan saukar shi daga mukamin ministan Abuja a 2015, sai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya wato EFCC ta fara tuhumarsa da zargin badakalar filaye ba bisa ka'ida ba a babban birnin kasar zamanin yana minista.

Bayan shafe watanni ana gudanar da bincike daga karshe da EFCC din ta kama shi a 2016, saboda zargin hannu a wata badakalar kudi.

Zamansa gwamna

A lokacin zabukan 2019 ne Bala Muhammad ya tsaya takarar gwamnan Bauchi karkashin jam'iyyar PDP kuma hukumar zaben Najeriya wato INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Wannan lamari ya sa EFCC ta dakatar da binciken da take masa saboda kariya da yake da ita a matsayinsa na gwamna kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada.

Bayan zuwa kotuna har uku kan kalubalantar sakamakon zaben da abokin takararsa Mohammed Abubakar ya yi a Kotun Sauraron Kararrakin Zabe da Kotun Daukaka Kara, a karshe Kotun Koli ta tabbatar wa da Bala Kaura nasararsa.

Asalin hoton, Bauchi State Government House

Bayanan hoto,

Gwamnan Bauchi Bala Muhammad