Ana bincike kan bullar zazzabin Lassa a Kano

Lassa Fever

Asalin hoton, Getty Images

Akalla mutum uku ne suka mutu a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano sakamakon kamuwa da wata cuta da ake kyautata zaton zazzabin Lassa ce.

Cikin wadanda suka mutun har da jami'an lafiya biyu a asibitin.

A wata sanarwa da ta fitar ta cikin gida, hukumar asibitin na AKTH ta sanar da fara gudanar da bincike kan wasu mutane da ake zargin sun kamu da cutar zazzabin na Lassa.

Sai dai har kawo yanzu hukumomin lafiya a Kano ba su tabbatar da barkewar cutar ba a hukumance. Amma wasu bayanai na wasu manyan jami'ai da masu ruwa da tsaki a asibitin na Malam Kano sun tabbatar wa BBc barkewar annobar.

An fara zargin barkewar annobar ne bayan wata jam'iar jinya ta mutu sakamakon zazzabi mai zafi, sanna wani likita shi ma ya mutu 'yan kwanaki kadan. Sai kuma wani ma'aikacin lafiyar da yanzu haka ke kwance yana karbar magani.

Duka jami'an dai sun yi mu'amala ne da wata mara lafiya da taje asibitin daga jihar Bauchi. Bayanai sun ce matar na dauke da juna biyu lokacin da ta je asibitin, kuma an yi mata tiyatar gaggawa ta cire cikin da take dauke da shi domin ceto rayuwarsu.

A yanzu haka dai haka asibitin na Malam Aminu Kano ya tsara gudanar da taron wayar da kan ma'aikatan asibitin game da hanyoyin da za su bi don kariya daga annobar a ranar Laraba.

Sanarwar da asibitin ya aike wa ma'aikatansa ta kuma bukaci ma'aikatan asibitin su kwantar da hankalinsu da kuma yin taka-tsantsan yayin da suke duba sauran marasa lafiya, kana su kuma kauce wa yada bayanai dangane da wannan batu a shafukansu na sada zumunta don kaucewa tayar da hankalin jama'a.

A shekarar 2016 ma jihar Kano ta kasance cikin jihohin kasar da suka yi fama da cutar ta zazzabin Lassa kafin daga baya a shawo kanta.

A yanzu haka dai kimanin jihohon Najeriya bakwai ne ke fama da annobar ta zazzabin Lassa.

Masana lafiya dai sun bayyana cewa zazzabin Lassa ba shi da magani, don haka ne hukumomi suke wayar da kai kan hanyoyin da za a bi domin kariya daga kamuwa da cutar mai saurin kisa.