Girgizar kasa ta kashe mutum 21

Bayanan bidiyo,

Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon bidiyon barnar da girgizar kasar ta yi

Akalla mutum 21 suka mutu, sama da mutum dubu kuma suka samu raunuka sakamakon wata girgizar kasa mai karfi a gabashin Turkiyya.

Girgizar kasar mai girman 6.8 ta faru ne a garin Sivrice da ke lardin Elazig inda girgizar kasar ta yi sanadiyar rushewar gine-gine da kuma tursasawa jama'a da dama garari kan tituna.

Rahotanni sun bayyana cewa an ji motsi ko kuma karamar girgizar kasa a Syria da Lebanon da kuma Iran da ke makwabtaka da kasar.

Tuni dama an saba samun girgizar kasa a Turkiyya inda a shekarar 1999 mutum 17,000 suka mutu a wata girgizar kasa mai karfi da ta faru a garin Izmit da ke yammacin kasar.

Girgizar kasar da ta faru a Turkiyya a ranar Juma'a ta faru ne da misalin karfe 17:55 agogon GMT.

Hukumar da ke bayar da gajin gaggawa da kuma lura da bala'i ta kasar ta bayyana cewa sama da masu bada agaji 400 ne aka tura yankin da abin ya faru dauke da gadaje da kuma tenti-tenti ga wadanda suka rasa muhallansu.

Asalin hoton, Reuters

Hukumar kuma ta yi gargadi ga wadanda lamarin ya shafa da kada su koma gidajensu domin gudun yiwuwar samun wata girgizar kasar da za ta iya biyo bayan ta farko da ta faru.

Hukumar ta bayyana cewa mutum 17 ne suka mutu a lardin Elazig sai kuma mutum hudu a jihar Malatya.

Sai dai tun da farkon faruwar lamarin gwamnan garin Malatya ya bayyana cewa mutum shida ne suka mutu a jihar