Kusan mutane 3000 sun kamu da Coronavirus

Coronavirus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A baya an zargi hukumomin kasar China da rufa-rufa a lokacin da sutar SARS ta bayyana tare da hallaka mutane da dama

Hukumomin kasar China sun tabbatar da cewa cutar Coronavirus ta hallaka mutane 80, kusan wasu 3,000 kuma sun kamu da cutar.

An dai kara hutun karshen shekarar gargajiya da kwanaki uku, a wani mataki na rage yaduwar cutar.

Tuni harkoki sun tsaya cak a birnin Wuhan da Hubei inda nan ne cutar ta fara bulla, ya yin da sauran biranen kasar suka sanya haramcin tafiye-tafiye.

Wani jami'in ma'aikatar lafiyar Chinaya ce a ranar Litinin adadin wadanda suka mutu a yankin Hubei ya karu daga mutum 56 zuwa 76, wasu hudu kuma sun mutu awani yankin na daban.

Yawancin wadanda suka mutu tsofaffi ne, da masu ciwon hakarkari.

A halin da ake ciki baki daya wadanda ma'aikatar lafiyar kasar ta tabbatar da kamuwa da cutar Coronavirus sun kai 2,744 ya yin da kafar yada labaran China ke cewa 300 daga ciki na cikin halin rai kwakwai-mutu-kwakwai.

Cutar ta yi nisan tafiya, an kuma samu mutane 41 da suka kamu da ita a kasashen Thailand, da Amurka da Australia sai dai har babu rahotannin mutuwar wani.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Cutar dai na haddasa ciwon hakarkari, da tushewar numfashi, da zazzafan zazzabi, Abin damuwar shi ne babu wata kwakkwarar allurer ragakafin kamuwa da ita.

Me ke faruwa a Wuhan da kewaye?

Birnin mai mutane miliyan 11 na cikin dokar ta baci, ta haramta tafiye-tafiye an kuma takaita zuruftun motoci akan tituna.

A iyakar yankin Hubei kuwa, ma'aikatan lafiya aka girke da ke binciken dumin jikin mutane kafin a bari su shiga yankin.

Shi kuwa ababban asibitin Wuhan ya cika makil da marasa lafiya, bangaren ayyukan gaggwa na asibitin babu masaka tsinke.

An girke sama da jami'an lafiya 500,000 dan yaki da cutar Coronavirus ta ke saurin yaduwa kamar wutar daji.

A Wuhan na sake gida asibitin wucin gadi guda biyu, manyan ma'aikatu na ta samar da abin rufe fuska da rigar kariya dga kamuwa da cutar.

Magajin garin Zhou Xianwang ya yi gargadin adadin wadanda ke kamuwa ya na karuwa cikin sauri sannan kusan mutane miliyan biyar da suka zo bukukuwan sabuwar shekara ne suka fice daga birnin Wuhan kafin a haramta shiga da fita.

Wanne hali ake ciki a China?

Tuni aka dakatar da shagulgulan bikin sanbuwar shekara a manyan biranen kasar hudu, da suka hada da Beijing, da Shanghai, da Xi'an da kuma Tianjin sannan an dakatar da sufurin motocin basbas na dogon zango..

Beijing kuwa ta rufe shahararren wurin yawon bude idon nan mai suna Forbidden City da wani bangare na Great Wall inda baki 'yan kasar waje da na kasar ke turuwa a lokaci irin wannan.

Yawancin biranen da ke gundumar Guangdong an ayyana dokar amfani da abin rufe fuska a bainar jama'a.

Ya yin da wuraren shakatawa na Disney da ke yankin Hong Kong da Shanghai an rufe su baki daya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Marasa lafiya sun cika sashen gaggawa na asibitocin da ke Wuhan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jami'an lafiya na feshin magani a wuraren da jama'a ke taruwa dan kariya daga yaduwar cutar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An haramtawa mutane zuwa kogin Yangtze mai launin ruwa kasa, da kogin Han mai launin sararin samaniya da ke Wuhan