'Yan Isra'ila za su fara zuwa Saudiyya

Benyamin Netanyahu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A baya dai babu wata huldar diflomasiyya tsakanin Saudiyya da Isra'ila

Isra'ila ta sanar da cewa za ta amince 'yan kasar su je Saudiyya a karon farko, a wani yunkuri da ake ganin na yaukaka dangantaka ne tsakanin kasashen biyu.

Sai dai kawo yanzu hukumomin Saudiyyar ba su fitar da sanarwa kan batun a hukumance.

Ministan cikin gida Aryeh Deri ya ce a yanzu Isra'ilawa mabiya addinin musulunci suna da damar yin balaguro zuwa saudiyyar ko dai tafiyar kasuwanci ta kwanaki 9, ko kuma gudanar da ayyukan ibada.

A baya dai kasashen Isra'ila da Saudiyya ba su da wata cikakkiyar alakar diplomasiyya tsakaninsu, sai dai a baya-bayan nan rahotanni sun bayyan acewa su na kokarin sasantawa dan yakar kasar Iran da suke yi wa kallon makiyarsu.

Masana irinsu Dr Tukur Abdulkadir na jami'ar jihar Kaduna, na ganin dalilan da suka sanya Isra'ila da Saudiyya ke kokarin yaukaka dangantaka tsakaninsu na da nasaba da yadda kasashen biyu ke kallon Iran a matsayin makiyarsu, sannan Saudiyya ba ta kallon Isra'ila a matsayin barazana idan a ka yi la'akari da yadda Iran da Amurka ke tashin hankali tsakaninsu.

Dr Tukur, na ganin wannan dangantaka ba za ta dore ba, ''idan aka yi la'akari da yadda siyasar gabas ta tsakiya ke tafiya, da kuma yadda 'yan boko a kasashen Larabawa ba sa son kwata-kwata a dawo da huldar diflomasiyya tsakanin kasashensu da Ira'ila, musamman kan yadda ta ke mamaye matsugunan Falasdinawa da kuma goyon bayan Amurka ta ke wannan mamaya, dan haka sabon kawancen ba bu inda zai je.''

Abin zuba ido a gani shi ne ko sauran kasashen Labarawa da ba sa ga maciji da Isra'ila za su bi yarima a sha kida a sabon kawancen da jagora a yankin gabas ta tsakiya ke shirin kullawa.