Buhari ya tura jiragen yaki don fatattakar barayin shanu a jihar Niger
Buhari ya tura jiragen yaki don fatattakar barayin shanu a jihar Niger
Ku latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraren hira da Garba:
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin sanya rundunar sojin sama ta kasar a aikin kai farmakin kan 'yan bindiga masu satar mutane da shanu a jihohin Naija da Kaduna da Zamfara.
A baya bayan nan dai ana ta kokawa da hare-hare da miyagun abubuwan da 'yan bindigar ke aikatawa ga alummomin jihar Naija.
Kakakin Shugaban Najeriyar, Mallam Garba Shehu, ya yi wa BBC karin bayani kan wannan batu: