Shahararren mai daukar hoton Afirka Ta Kudu ya rasu

Santu Mofogeng

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Santu Mofogeng ya shahara wajen daukar hoto a Afurka ta Kudu

Ana ci gaba da alhinin mutuwar shaharren mai daukar hoton nan dan Afirka Ta Kudu Santu Mofogeng, wanda ya rasu yana da shekara 64 a duniya.

An haifi Mofokeng a Soweto, inda ya fara sana'ar daukar hoto tun yana dan karaminsa a gefen hanya, kafin daga bisani ya shahara aka san da zamansa a daukacin kasar kan rawar da ya taka a yaki da wariyar launin fata.

A shekarar 1985 ne Mista Mofogeng ya kafa wata kungiya mai suna Afrapix, kungiyar da ta karya lagon tsangwamar 'yan jarida lokacin yaki da wariyar launin fata.

Kungiyar da Santu Mofogeng ke jagoranta ce take samarwa jaridun Afirka Ta Kudu hotunan da suke amfani da su marasa kala, wadanda da wuya ka gan su a jaridun da ake saidawa a yankunan da Turawa farar fata suka mamaye.