Turmutsutsi ya kashe 'yan makaranta 14 a Kenya

Iyaye da 'yan uwan dalibai sunyi cirko-cirko a asibiti

Asalin hoton, NATHAN OCHUNGE

Bayanan hoto,

Iyaye da 'yan uwan dalibai sunyi cirko-cirko a asibiti

Akalla dalibai 14 ne su ka mutu a wani turmutsusti da ya faru a wata makarantar firamare da ke arewacin Kenya.

Lamarin ya faru a makarantar firamare da ke Kakamega ranar Litinin.

Rahotanni sun ce daliban na barin azuzuwansu da misalin karfe biyu a lokacin da abun ya faru.

Ministan ilimin Kenya George Magoha ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa gwamnatin kasar na cike da alhini tana kuma jajanta wa iyayen yaran.

Baya ga yara 14 da su ka mutu rahotanni sun tabbatar da cewa kusan 40 sun jikkata, kuma yanzu haka suna karbar magani a asibiti.

Kawo yanzu ba a iya gano musabbabin faruwar turmutsutsin ba.

Kwamandan rundunar 'yan sanda Kakamega David Kabena ya ce ana kan bincike.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Tuni an fara binciken musabbabin turmutsutsin a makarantar firamare da ke Kakamage

Sai dai wata majiya na cewa 'yan makarantar na kokarin saukowa da ga matakalar bene ne yayin da ya karyo da su.

Hakama rahotannin sun ce wasu daga cikin yaran sun ruguzo daga hawa na uku a kokarin gudu.

Hakama hotunan bidiyo sun nuna jama'a cirko cirko a asibitin da ake duba yaran.

Bayanan hoto,

Ko a watan Satumban 2019 'yan makaranta takwas sun mutu bayan da rufin aji ya rufta musu

Tuni an fara tambaya kan irin matakan kariya ga 'yan makaranta a Kenya don gujewa faruwar irin wannan ibtila'i.

Ko a watan Satumban bara yara takwas sun mutu kuma wasu 69 sun jikkata a lokacin da rufin wani aji ya afka kansu a Nairobi.