Iran ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa saboda leken asiri

A

Asalin hoton, EPA

Kotun Kolin Iran ta tabbatar da hukuncin kisa ga wani mutum da aka samu da laifin yi wa hukumar CIA aikin leken asiri.

Amir Rahimpour "ya samu makudan kudade" don bai wa Amurka bayanai game da shirin nukiliyar Iran, a cewar mai magana da yawun ma'aikatar shari'a Gholamhossein Esmaili.

Ya kara da cewa an yanke wa "wasu karin Amurkawa biyu" hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 10 saboda leken asiri, da karin shekara biyar saboda yi wa tsaron kasa barazana.

Sai dai Mr Esmaili bai bayyana sunayensu ba.

Kawo yanzu, gwamnatin Amurka ko CIA ba su ce komai ba game da batun.

Amma a watan Yuli, jami'an Amurka sun bayyana kokonto kan sanarwar da Iran ta yi cewa ta kame masu leken asiri 17 da ake zarginsu da kwasar bayanai game da shirin nukiliyar kasar da sojojin kasar suna mika wa CIA.

Ma'aikatar ta ce an yanke wa wasu daga cikinsu hukuncin kisa.

"Yana daga cikin dabi'ar Ayatollah yi wa duniya karya," a cewar Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yana inkiya ga Shugaban Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei."

A makon da ya gabata ne aka zartar da hukuncin kisa kan wani tsohon dan kwangilar ma'aikatar tsaron Iran, Jalal Hajizavar bayan da aka same shi da yin leken asiri.

Bayanai sun ce Hajizavar ya taba amsa cewa biyansa aka yi ya yi wa CIA leken asiri.

A 2016 kuma, Iran ta rataye wani kwararre kan harkar nukiliya da aka samu da laifin yi wa Amurka leken asiri.

Rahotanni sun ce Shahram Amiri ya koma Amurka a 2009, amma ya koma Iran a 2010 bayan ya yi ikirarin cewa an yi garkuwa da shi tare da tsare shi ba da son ransa ba.

Labarin tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke wa Amir Rahimpour na zuwa ne a dai-dai lokacin da dangantaka tsakanin Iran da Amurka ta yi tsami.

A Janairu ne wani babban kwamandan sojin Iran Qasem Soleimani ya mutu sakamakon wani hari da Amurka ta kai a Bagadaza da jirgi mara matuki.

A wani mataki na mayar da martani, Iran ta harba makamai masu linzami kan sansanonin dakarun Amurka a Iraki.