Kalaman Abidal sun fusata Messi

Lionel Messi
Bayanan hoto,

Yarjejeniyar Lionel Messi da Barcelona za ta kare a karshen kakar wasannin bana

Daraktan wasannin Barcelona Eric Abidal ya bulguta cewa kungiyar za ta yi iya kokarinta na ganin ta sayi dan wasan gaban Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang.(Mirror).

Rahotanni sun ruwaito cewa Lionel Messi ya mayar wa Abidal da martani, bayan da ya bayyana cewa 'yan wasa sun taka rawa wurin sallamar tsohon mai horar da 'yan wasan kungiyar Enersto Valvede.

Manchester City ta ce ta shirya tsaf don taya Lionel Messi matsawar dan wasan ya zabi kawo karshen zamansa a Barcelona, yayin da yarjejeniyarsa ta kare a karshen kakar wasannin bana.(Manchester Evening News).

Wolves ta bayyana cewa a shirye take ta kulla yarjejeniyar din-din-din da Adama Traore da a yanzu ke zaman aro a kungiyar.(Telegraph).

Chelsea da Manchester za su gwabza wurin neman kawo dan wasan gaban Borussia Dortmund Jadon Sancho.(Sun).

Hakama kungiyoyin biyu za su fafata wurin kulla yarjejeniya da dan wasan gaban Lyon da Faransa Moussa Dembele. (Mirror).

Tsohon dan wasan tsakiyar Tottenham Christian Eriksen ya ce am maida shi saniyar ware a kungiyar tun bayan da bayyana ra'ayinsa na barin kungiyar.

Bayanan hoto,

Eric Abidal

Dan kasar Denmark din a yanzu na wasa ne a Inter Milan na Italiya.

Ana rigagen kulla yarjejeniya da matashin dan wasan gaban Bayern Leverkusen na Jamus Kai Havertz a tsakanin Liverpool da Manchester United.(Mirror).

Ita kuwa Manchester City na fuskantar kalubale wurin ganin ta hana Leroy Sane barin kungiyar zuwa Bayern Munich, yayin da dan wasan ya canza Ejan din sa.(Telegraph).

Akwai yiwuwar Barcelona ta kulla yarjejeniya da dan wasan gaban Getafe Angel Rodriguez don maye gurbin Ousmane Dembele na wucin gadi, kafin ya dawo jinya.(Marca).