An kashe mutane, an kona gidaje a rikicin Kazakhstan

@

Asalin hoton, Getty Images

An kashe mutum takwas tare da jikkata fiye da mutum 20 a wata tashin-tashina da aka yi a wani kauye ranar Juma'a a kasar Kazakhstan.

Rahotanni sun ce an cinna wa gidaje da shaguna fiye da 45 wuta a lokacin rikicin kabilancin.

Rikicin ya barke ne tsakanin 'yan kabilar Dungan da Musulmai 'yan kabilar Hui da suka yi gudun hijira daga China a cikin karni na 19.

Shugaban kasar Kassym-Jomart Tokayev ya ce 'yan sanda na tsare da 47 da ake zargi suna da hannu a fadace-fadacen da ake yawan samu tsakanin mazauna yankin.

Shugaban Kassym-Jomart ya shaida wa 'yan jarida cewa kura ta lafa, kuma ya umurci jami'an tsaro da su dauki matakan hana sake aukuwar hakan.

Ya ce jami'an tsaron za su gurfanar da masu yada labarun karya da kalaman nuna tsana da na tunzura a gaban kotu.

Hotunan rikicin da aka yada a kafafen zumunta a ranar Juma'a sun nuna wasu matasa dauke da makamai na cinna wuta a kan gine-ginen da ke kan hanyar kauyen.

Ministan yada labaran kasar ya ce rikicin na da nasaba da fadace-fadacen da ake samu a yankin.