Buhari ya caccaki shugaban Dattawan Arewa Ango Abdullahi

Buhari

Asalin hoton, BUHARI SALLAU/FACEBOOK

Bayanan hoto,

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya caccaki shugaban kungiyar Dattawan Arewacin kasar, Farfesa Ango Abdullahi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Femi Adesina, ya fitar ranar Lahadi ya ce Ango Abdullahi ba shi da wata kima kuma kusan shi kadai ne yake kidansa ya yi rawarsa a Kungiyar Dattawan.

A cewarsa, "Ranar Lahadi Farfesa Ango Abdullahi ya sanya hannu a kan wata sanarwa da ta tabo batutuwa da dama game da arewaci da ma Najeriya baki daya.

Tsohon shugaban jami'ar ya sanya hannu kan takardar ne a madadin Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya.

Amma a hakikanin gaskiya, Ango Abdullahi shi ne kadai a kungiyar. Kungiya ce da ba ta da wata martaba. A iya cewa shugabanta kamar soja ne da ba shi da dakarun da ke bin sa."

Mr Adesina ya ce tun gabanin zaben 2019 Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta nuna rashin kaunarta ga Shugaba Buhari, sannan ta bayyana dan takarar da take goyon baya.

Ya kara da cewa gwamnatin Buhari ba ta bukatar mutane irinsu Farfesa Abdullahi don gaya mata yadda za ta tafiyar da harkokin kasar.