Gwamnonin Najeriyar da suka je Kotun Koli da kafar dama a 2020

Hukunce-hukuncen da kotun koli ta yanke a kan zabukan gwamnonin jihohi a Najeriya sun bar wasu 'yan takara da magoya bayansu cikin tagumi yayin wasu ke farin ciki.
Masu korafi a kan sakamakon zabukan da hukumar zaben Najeriya INEC ta bayyana sun shigar da kara a gaban kotunan sauraren kararrakin zabe, tare da daukaka kokensu zuwa kotun daukaka kara har zuwa kotun koli domin neman adalci.
Hukuncin kotun koli shi ne na karshe kuma daga shi babu wata dama ta daukaka kara sai dai hakuri.
Diri Duoye - Bayelsa
Asalin hoton, @OfficialPDPNig
A baya-bayan nan alkalan kotun kolin Najeriya karkashin mai shari'a Mary Odili sun sauke David Lyon na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa.
Ana ganin wannan matakin na nufin Diri Duoye da jam'iyyarsa sun tsinci dami a kala ne a ranar 13 ga watan Fabrarirun 2020 a jajibirin rantsar da Mista Lyon a matsayin gwamnan jihar.
Amma saboda rashin cikakken sakamako, babu wanda ya tabbatar da abin da zai faru a Bayelsa, ganin cewa kotun ba ta fayyace dukkan batutuwan da suka shafi shari'ar ba.
A baya kotun daukaka kara ta tabbatar da Lyon a matsayin zababben gwamnan jihar kamar yadda hukumar zabe ta bayyana cewa shi ne ya yi nasara a zaben ranar 16 ga watan Nuwamban 2019.
Da yake karanta hukuncin kotun kolin mai shari'a Ejembi Eko ya ce kotun ta soke zaben Lyon ne saboda mataimakinsa Biobarakuma Degi-Eremienyo ya bayar da takardun karya ga INEC domin samun tsayawa takara.
Alkalan sun soke kuri'un da Lyon da Degi-Eremienyo na jam'iyyar APC sannan suka ayyana jam'iyyyar da ta fi samun kuri'un da ake bukata a zaben a matsayin wadanda suka yi nasara.
Kotun kolin ta kuma umurci INEC ta soke shaidar cin zaben da ta ba wa David Lyon da mataikinsa.
Sai dai kawo yanzu hukumar zabe a Najeriya na dakon cikakken hukuncin da kotun kolin ta gabatar domin sanin mataki na gaba - wanda shi ne ta mika wa dan takarar jam'iyyar PDP shaidar lashe zaben - ko kuma tasake gudanar da wani zaben nan ba da jimawa ba.
A watan Nuwambar 2019 ne INEC ta ayyana Lyon na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar, bayan ya samu kuri'u 352,552.
INEC ta kuma bayyana Douye Diri na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya zo na biyu da yawan kuri'a 143,172.
Hope Uzodinma - Imo
Asalin hoton, @Govhopeuzodinma
Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo
Murna ta koma ciki a wurin jam'iyyar PDP da tsohon gwamnan jihar Emeka Ihedioha, bayan kotun koli ta soke zabensa da aka yi a ranar 9 ga watan Maris din shekarar 2019.
A hukuncin da ta yanke a ranar 14 ga watan Janairun 2020, Kotun Kolin ta ba da umurnin a rantsar da Hope Uzodinma na jam'iyyar APC washegari, a matsayin zababben gwamnan Imo.
Rudani
Hukuncin kotun kan zaben na Imo ya daure wa 'yan kasar da dama kai, musamman 'yan siyasa da ke ganin akwai bukatar Kotun Kolin ta sake zanari a kan hukuncin.
Masu kokwanto a kan hukuncin na ganin Kotun Kolin ta yi kuskure wajen bayyana yawan kuri'un da ta bayyana a matsayin adadin da mayan 'yan takarar suka samu a zaben.
Daga cikinsu akwai masu cewa yawan kuri'un da kotun ta bayyana ya wuce wanda INEC ta bayyana a matsayin wadanda aka jefa a zaben.
Jam'iyyar ta yi zanga-zangar kin amincewa da hukuncin wanda ta ce yana cike da kurakurai, tare neman kotun ta gyara hukuncin da ta yanke kan zaben na gwamnan jihar Imo.
PDP na ganin hukuncin barazana ce ga dimokradiyyar kasar, kuma yana iya sa jama'a su yanke kauna ga tsarin shari'ar kasar.
"Kuri'un da aka tantance kafin zaben ba su kai yawan wadanda kotun ta ce an kada ba, wannan kadai ya isa jefa shakku a zukatan jama'a," a cewar Sakataren jam'iyyar na kasa, Sanata Umar Tsauri.
Amma wani masanin shari'a, Barrister Bulama Bukarti, ya ce "Idan kotun koli ta yanke hukunci to ya zauna kenan, dalili kuwa shi ne dole ne ya kasance shari'a tana da iyaka, idan ba haka ba kenan za a yi ta shari'a ne shekara da shekaru babu iyaka, don haka hukuncin ya zauna''.
Abdullahi Ganduje - Kano
Asalin hoton, @dawisu
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Shi ma gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tsallake siradi bayan Kotun Koli ta yi watsai da karar jam'iyyar PDP da dan takarar gwamnanta a jihar Abba Kabiru Yusuf a zaman kotun na ranar 20 ga watan Janairun 2020.
Abba da jam'iyyar Kano sun daukaka kara zuwa kotun koli ne bayan Ganduje da jam'iyyarsa ta APC sun yi nasara a kotun sauraren karar zabe a Kano da kotun daukaka kara da ke zamanta a Kaduna.
Alkalan kotun sun tabbatar da nasarar Ganduje a zaben kamar yadda INEC ta bayyana kuma hukuncin sauran kotunan suka tabbatar.
A ranar 12 ga watan Afrilun 2019 ne PDP da Abba suka shigar da kara a kotun sauraron kararrakin zaben jihar tana kalubalantar sakamakon zaben da INEC ta sanar cewa Ganduje ya yi nasara.
Jam'iyyar adawar na ikirarin dan takararta ne ke da mafi yawan kuri'un da aka jefa a zaben ranar 9 ga watan Maris, da aka kammla a ranar 23 ga watan Maris na 2019.
Bayan sanar da sakamakon zagayen farko na zaben wanda Abba ke kan gaba, an gudanar da karashen zaben a ranar 23 ga watan na Maris inda INEC ta sanar da Ganduje a matsayin wanda ya yi nasara.
Aminu Tambuwal - Sokoto
Asalin hoton, @AWTambuwal
Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal (sanye da fararen kaya)
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambauwal na daga cikin wadanda suka yi nasara a Kotun Koli wadda ta tabbatar da nasararsa a zaben gwamnan jihar na 2019.
Tun da farko Tambuwal ya samu nasara a kotu sauraren karakin zaben gwamnan jihar Sokoto, da kuma kotun daukaka kara a Kaduna.
Kotunan biyu sun yi watsi da karar da dan takarar jam'iyyar APC Ahmed Aliyu ya shigar na kalubalantar nasarar Tambuwal na jam'iyyar PDP a zaben.
A zamanta na ranar Litinin 20 ga watan Janairu 2020, Kotun Koli ta yi watsi da karar da jam'iyyar APC da dan takar gwamnanta a jihar Sokoto Ahmed Aliyu suka shigar a gabanta, suna kalubalantar nasarar Tambuwal zaben gwamnan jihar.
INEC ta sanar da Tambuwal a matsayin wanda ya nasara a zaben gwamnan jihar Sokoton bayan ya samu kuri'a 512,002.
Hukumar ta ce Tambuwal ya doke babban abokin hamayyarsa, Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC wanda ya zo biyu da yawan kuri'u 511,660.
Simon Lalong - Filato
Asalin hoton, THE GUARDIAN
Gwamna Simon Bako Lalong na jihar Filato
Nasarar gwamna Simon Lalong na jihar Filato ta tabbata a Kotun Koli bayan alkalan da suka saurari karar sun yi watsi da zargin magudin da babban abokin hamayyarsa Jeremiah Useni na jam'iyyar PDP suka yi.
Kotun ta tabbatar da zaben da Simon Bako Lalong na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar, saboda masu karar sun kasa gabatar da hujjojin da za su gamsar da kotun a kan zargin.
Bala Muhammad - Bauchi
Asalin hoton, @dawisu
Bala Muhammad, Gwamnan jihar Bauchi
A kan zaben Bauchi kuma, Kotun Koli tabbatar da dan takarar jam'iyyar PDP Bala Muhammad ta yi a matsayin gwamnan jihar.
Hakan ya faru ne a ranar 20 ga watan Janairun 2020 bayan alkalan kotun sun yi ittifaki wajen watsi da karar da tsohon gwamnan jihar Muhammad Abdullahi Abubakar ya shigar yana kalubalantar nasarar Bala Muhammad a zaben.
Muhammad Abubakar ya daukaka kara zuwa Kotun Kolin ne a zargin da ya yi na cewa an tafka magudi a zaben da INEC ta bayyana Bala Muhammad a matsayin wanda ya samu nasara.
Nasir El-Rufai - Kaduna
Asalin hoton, @elrufai
Gwamna Kaduna, Nasir El-Rufai
Kafin nan, a karshen shekarar 2019 ne gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya samu nasara a Kotun Koli a kan Isah Muhammad Ashiru da jam'iyyar PDP da ke kalubalantar nasarar El-Rufai a zaben gwamnan jihar na ranar 9 ga watan Maris na 2019.
A zaman kotun na ranar 18 ga watan Disamban 2019, alkalai bakwai na kotun da Mai shari'a Mary Odili ta jagoranta suka tabbatar da zaben El-Rufai a matsayin gwamnan jihar ta Kaduna.
AA Sule - Nassarawa
Asalin hoton, @NasarawaGovt
A ranar ne kuma Mai Shari'a Mary Peter-Odili ta yi watsi da daukaka karar da David Ombugadu na jam'iyyar PDP ya yi na kalubalantar zaben Gwamna Abdullahi A. Sule na jihar Nassarawa.
Alkalan sun ce mai daukaka karar da jam'iyyarsa ta PDP ba su da kwararan hujjoji.
Aminu Masari - Katsina
Asalin hoton, @GovernorMasari
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina
Kotun ta kuma tabbatar da nasarar gwamnan jihar katsina Aminu Bello Masari da Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas bayan ta yi watsi da kararrakin da aka shigar na kalubalantar zabensu.
Seyi Makinde - Oyo
Asalin hoton, @seyiamakinde
Seyi Makinde, Gwamnan jihar Oyo
Kotun ta kuma tabbatar da nasarar Seyi Makinde a zaben gwamnan jihar Oyo, bayan ta yi watsi da hukuncin kotun daukaka karar da ta soke hukuncin da kotun sauraren karar zaben gwamnan jihar.
Ta yi watsi da karar ne, wadda jam'iyyar APC da dan takararta Adebayo Adelabu suka shigar.
Kotun daukaka karar ta ce kotun sauraren kararrakin zaben ta yi kuskure wajen yin watsi da korafin jam'iyyar APC, amma ta ki tsige Makinde a matsayin gwamnan Oyo.
Amma Kotun Koli ta soke hukuncin.
Babajide Sanwolu - Legas
Asalin hoton, @jidesanwoolu
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwolu
Alkalan Kotun Kolin sun kuma yanke hukuncin da ke tabbatar da Babajide Sanwolu a matsalyin zababben gwamnan jihar Legas.
Kotun ta yi watsi da kararrakin da aka shigar masu kalubalantar nasarar Sanwolu a zaben gwamnan jihar.