An sa dokar hana fita a Bayelsa

Rundunrnar 'yan sandan jihar ce ta bayyana haka a ranar da aka rantsar da sabon gwamnan Hakkin mallakar hoto POLICENG/TWITTER
Image caption Rundunrnar 'yan sandan jihar ce ta bayyana haka a ranar da aka rantsar da sabon gwamnan

An sanya dokar hana fita ta kwana uku a jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya jim kadan bayan rantsar da sabon gwamnan jihar Douye Diri.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Uche Anozia, ya ce dokar za ta fara aiki daga karfe 8 na dare zuwa karfe 6 na safe daga ranar Juma'a 14 ga watan Fabrairu zuwa ranar Lahadi.

Hukumomin tsaro a jihar sun sanar da kafa dokar ne bayan gwamna Douye Diri ya sha rantsuwar fara aiki bayan ya karbi takardar shaidar cin zaben gwamna daga hukumar zaben kasar INEC.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce an kafa dokar ne sakamakon tashin hankali da aka samu a Yenagoa, babban birnin jihar, bayan INEC ta ba wa gwamnan takardar shaidar cin zabe.

INEC ta ba wa Douye Diri na jam'iyyar PDP shaidar cin zaben ne bisa umurnin Kotun Koli.

A zamanta na ranar Alhamis 13 ga watan Fabrairu, Kotun Kolin ta soke zaben David Lyon na jam'iyyar APC, sannan ta umarci INEC da ta ayyana wanda ya fi samun yawan kuri'u a matsayin zababben gwamnan jihar.

'Hukuncin Kotun Kolin ya fusata wasu mazauna jihar wadanda suka yi ta tayar da hankalin jama'a', a cewar kwamishinan.

Kwamishinan 'yan sanda ya ce jami'an runduar sun tsare wasu mutun 8 da zargin hannu a tashin hankalin da ya yi sanadiyyar asarar dukiyoyi a Yenagoa.