UEFA ta dakatar da Manchester City daga gasar Turai

Manchester City na da wasa 10 da za ta buga a gasar Premier Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester City na da wasa 10 da za ta buga a gasar Premier

Hukumar kwallon kafa ta UEFA dakatar Manchester City daga shiga gasar zakarun Turai na kaka biyu saboda aikata wasu laifuka.

UEFA ta kuma sanya tarar Yuro miliyan 30 a kan Manchester City mai rike da kambin gasar Premier.

Hukuncin a cewar hukumar ya biyo bayan samun kungiyar da laifin saba ka'idojin da suka dangance bayyana kudaden da kungiyar ta samu daga tallace-tallace da masu daukar nauyi.

Kungiyar za ta kara da Real Madrid a zagayen farko na gasar Champions League wanda za a fara karawa a ranar 26 a Bernabeu.

City ta bayyana takaicinta kan hukuncin amma ta ce bata yi mamaki kuma za ta daukaka kara domin neman adalci.

Hukumar kula da harkokin kudade na CFCB ya ce City ta yi kari a bayanan da ta gabatar wa Uefa na kudaden da take samu daga tallace-tallace da masu daukar nauyi daga 2012 zuwa 2016.

CFCB ta kuma zargi kungiyar da kin ba da hadin kai a lokacin gudanar da bincike.

Amma a sanarwar da ta fitar, City wadda ke da damar daukaka kara, ta yi zargin rashin adalci a hukucin.

Kungiyar ta ce "A 2018 babban jami'in binciken Uefa ya gabatar da sakamo da kuma hukuncin da ya ke son a yi wa kungiyar, tun ma kafin a fara gudanar da bincike."

Don haka ta ce za ta daukaka kara domin neman adalci saboda tun da farko jami'in ya riga ya bayyana ba zai yi adalci ba.