Kotu ta soke auren Musulunci saboda saba dokar kasa

@

Asalin hoton, Getty Images

Kotu ta warware auren Musuluncin bayan ta soke hukuncin kotun da ta tabbatar da halascin auren a Birtaniya.

An daura auren Mohammed da Nasreen masu 'ya'ya hudu yanzu ne a birnin Landan a shekarar 1998 a gaban wani limami da shaidu 150.

Yanzu shekara biyu ke nan Nasreen na neman rabuwa da Mohammed din a gaban kotu amma ya dage cewa da ma can babu aure a tsakaninsu tunda ba bisa dokar kasar aka yi ba.

Hakan ya biyo bayan wata takaddama da ta sa Nasreen mijin nata ba sa zama tare da juna tun shekarar 2016.

Da farko wata kotu ta yanke hukunci cewa auren Musuluncin da aka daura musu halastacce ne domin ya dace da dokokin aure na Birtaniya.

Amma kotun daukaka kara ta soke hukuncin na 2018, tare da ayyana auren Musuluncin wa Nasreen da Mohammed a matsayin haramtacce wanda ya saba doka.

Alkalan kotun sun ce shirin ma'auratan na sake yin biki bisa tanadin dokar kasar ya tabbatar da cewa ma'auratan sun yarda auren Musuluncin da aka daura musu ba karbabbe ba ne.

Antoni janar din kasar ya yanke hukuncin ne a kan shari'ar Nasreen Akhter da mijinta Mohammed Shabaz Khan, 'ya'ya hudu.

Bayan daurin auren Mohammed da Nasreen, amaryar ta sha nuna damuwa da neman a gudanar da shagalin bikin kamar yadda dokar kasar ta tanada.

A shekarar 2016 suka rabu da juna, kuma Mohammed ya yi kokarin matar na neman saki na tsawon shekara biyu, bisa hujjar cewa ba su taba yin aure da juna ba, a idon doka.

Amma matar ta ce aurensu na Musulunci halastacce ne, kuma tana da hakkin ta bukaci rabuwa da Mohammed kamar yadda dokar kasar ta yi tanadi ga halastattun ma'aurata.