Shugaban Facebook na son a tsaurara dokokin kafafen zumunta

Shugaban Facebook Mark Zuckerberg na jawabi a gaban wani kwamiti

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Facebook na fuskantar karin matsin lamba a kan ya magance matsalar labarun karya a intanet

Facebook na neman a kara yin dokokin haramta sakonni masu cutarwa a intanet. Shugaban Facebook Mark Zuckerberg ya ce kamfanonin sada zumunta irin nasa ba su ne ke da alhakin kayyade mene ne halastaccen 'yancin fadar albarkacin baki ba.

Manyan kamfanonin sada zumunta irin Facebook na kara fuskantar matsin lamba cewa su magance matsalar yada bayanan kanzon kurege a intanet.

Da yake jawabi a wani taro da aka gudanar a kasar Jamus kan harkokin tsaro, Mark Zuckerber ya ce tsananta dokoki na iya kaiwa ga tauye 'yancin bayyana ra'ayi.

An sha sukan Facebook musamman a kan tsarinsa na tallace-tallacen siyasa. A shekarar 2018 kamfanin ya fito da sabbin tsare-tsare a kan tallace-tallacen siyasa a Amurka. A 2019 kuma ya fara amfani da tsare-tsaren a sauran kasashe.

Dokokin sun hada da bayyana sunan masu daukar nauyin tallace-tallacen tare da ajiye kwafen tallace-tallacen a ma'ajiyar bayanai da kowa zai iya samu har na tsawon shekara bakwai.

Amma a wannan makon kamfanin ya ce ba zai rika sanya sakonnin siyasa da taurarin shafukan sada zumunta suka dauki nauyi a ma'ajiyar bayanan nasa ba.

Haka kuma tsarin bai kunshi cewa sai kamfanin ya rika tantance sahihancin bayanan da ke cikin sakonnin da 'yan siyasa ke wallafawa a koyaushe ba.

Zuckerber ya shaida wa taron cewa yana goyon bayan a yi dokoki.

"Ba ma son kamfanonin 'yan kasuwa su rika yanke hukunci game da samar da daidaito a zamantakewar jama'a ba tare da yin haki bisa tsarin na demokradiyya ba," inji shi.

Da ya ke jadddada bukatar gwamnatoci su yi sabbin dokoki a kan kafafen sada zumuta, Zuckerbeg ya ba ce ya kamata dokokin hanyoyins sada zunta su hada dokokin kafafen yada labarai da na sadarwa.

"Amma tunda babu irin wadannan dokokin, za mu ci gaba da yin iya kokarinmu," a Zuckerberg.

Facebook ya kuma amince da zargin da ake masa na jan kafa wurin daukar mataki a kan wanzuwar hukumomi da suka yi kaurin suna kan yada bayanan karya ta intanet, irinsu Rasha.

Ya kara da cewa wasu miyagu na kara fito da hanyoyin na batar da sahunsu ta hanyar boye adireshin masu amfani da shafukan.

Asalin hoton, Reuters

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Domin a magance hakan, Facebook ya ce ya kafa tawaga mai mutun 35,000 da za su rika lura da sakonni da harkar tsaro a kan manhajarsa.

Kamfanin na kuma rufe shafukan bogi fiye da miliyan daya da ke kan manhajarsa a kullum, tare da taimakon kungiyar Amnesty International, inji shi.

"Abin da muke kashewa yanzu ya fi yawan kudaden shigar da kamfanin ke samu a sadda muka fara sayar da hannun jari a shekarar 2012, lokacin da mutum biliyan daya ke amfani da shafinmu," Zuckerberg ya yi karin haske.

A ziyarar da ya kai Turai din, Zuckerberg zai gana da 'yan siyasa da jami'in gwamnati a biranen Munich da Brussels a kan batutuwan da suka shafi dokoki da sarrafa bayanai da kuma haraji.

Duk da sukar da ya sha a kan tallace-tallacen siyasa, kamfanin Facebook ya ce masu amfani da manhajojinsa - Facebook da Messenger da Whatsapp da Instagram - na ci gaba da karuwa.

A farkon watan Fabrairun 2020, kamfanin ya ce mutum biliyan biyu ne ke amfani da manhajarsa ta Whatsapp, sama da kashi daya bisa hudu na yawan al'ummar da ke a fadin duniya.