Kotun Koli ta dage sauraren karar zaben Imo da Zamfara

CJN
Bayanan hoto,

Mai Shari'a Tanko Muhammad

Kotun kolin Najeriya ta dage kararrakin da aka shigar gabanta wadanda ke kalubalantar hukuncin kotu na korar tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha daga kan kujerarsa da kuma soke nasarar da jam'iyyar APC ta samu a zabukan 2019 da aka gudanar a matakai daban-daban a jihar Zamfara.

Kotun ta dage karararrakin ne zuwa ranar biyu ga watan Maris na 2020.

Lauyan Ihedioha da PDP, Kanu Agabi mai mukamin SAN ya nemi a dage karar domin bai wa bangarorin damar kammala shirye-shirye.

Lauyan Uzodinma da APC, Damian Dodo SAN bai kalubalanci rokon PDP ba.

Alkalin alkalan kasar Mai shari'a Tanko Muhammad ya jagoranci alkalai bakwai a sauraron karar ta Ihedioha da mambobin APC a Zamfara kan kalubalantar hukuncin kotun.

Sauran mambobin sun hada da Mai shari'a Sylvester Ngwuta da Kayode Ariwoola da Kudirat Kekere-Ekun da Inyang Okoro da Amina Augie da kuma Uwani Abba-Aji.

A ranar 14 ga watan Janairun bana ne tawagar lauyoyi bakwai karkashin alkalin alkalai suka tsige Ihedioha daga kan kujerarsa ta gwamnan Imo tare da ayyana Hope Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mai shari'a Kekere-Ekun wanda ya karanta hukuncin kotun ya tabbatar da karar da Uzodinma ya daukaka sannan kuma ya ce an tsame kuri'un da aka samu a mazabu 388 cikin 3,523 a sakamakon karshe na zaben da hukumar zaben kasar INEC ta sanar a jihar.

Kotun kolin ta ce Uzodinma shi ne halastaccen wanda ya ci zabe bayan an kara kuri'un da tun farko ba a hada da su ba.

Amma Ihedioha ta hannun lauyansa Chief Kanu Agabi SAN a ranar biyar ga watan Fabrairu ya shigar da kara gaban kotun inda ya nemi a soke hukuncin da aka yanke na ranar 14 ga watan Janairu.

Matakin kotun dai ya janyo cece-kuce a tsakanin jama'ar kasar har babbar jam'iyyar adawa PDP ta nemi kotun ta sake nazari kan hukuncin da ta yanke na korar Emeka Ihedioha.

Game da batun Zamfara kuwa, kotu tun a baya ta ce APC a jihar ba ta gudanar da zaben fitar da gwani bane

Kotun kolin ta ce jam'iyyar ba ta da halaltattun 'yan takara don haka ba za ta iya kasancewa wadda ta lashe zabukan jihar ba.

Tun farko dai Sanata Kabiru Marafa ne ya fara shigar da kara a gaban kotu, inda ya kalubalanci zaben fidda gwanin da APC ta yi.

Sai dai tun bayan da kotun kolin ta yanke hukuncin, tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari ya amince da hukuncin inda ya amince cewa jam'iyyar ta tafka kura-kurai a zaben da ta gudanar.