Ana bikin ranar harshen uwa ta duniya

  • Daga Nabeela Mukhtar Uba
  • Broadcast Journalist
Bayanan bidiyo,

Ranar harshen uwa ta duniya: tambayoyi a harshen Hausa

21 ga watan Fabrairun kowace shekara rana ce da aka kebe domin bikin harshen uwa a fadin duniya.

Kasar Bangladesh ce ta fara bijiro da maganar ranar harshen uwa ta duniya amma a 17 ga Nuwamban 1999 ne Hukumar Raya Ilmi da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO, ta fara sanar da ranar.

Daga bisani kuma Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita a hukumance.

Majalisar Dinkin Duniya ta kuma ayyana 2008 a matsayin shekarar harsuna a duniya domin inganta hadin kai da fahimta.

Ana fatan ranar, wadda jigonta shi ne "Harsunan da ba ruwansu da iyaka", za ta taimaka wajen habaka musayar yawu don samar da zaman lafiya da tabbatar da cewa ana damawa da kowa a al'umma.

Harshe dai yana da matukar amfani ga al'umma ta fuska da dama - hulda da ilimi da ci gaba, sai dai saboda ci gaban da ake samu a duniya, harsuna na fuskantar barazana.

Muhimmancin Ranar

An ware ranar domin bunkasa harsunan duniya da raya al'adu a tsakanin al'umma.

Shugaban sashen kimiyyar harsuna a Jami'ar Bayero da ke Kano Dr. Isa Yusuf Chamo ya ce an ware ranar "domin fadakar da mutane game da muhimmancin harsuna da al'adu mabanbanta."

Ya bayyana cewa a ranar ce ake tunatar da mutane muhimmancin adana harsunan.

"Harshe shi ne makamin ko wane bil'adama, duk wanda ya bar harshensa ya mutu, kusan ya kashe kansa da kansa."

"Domin harshe shi ne yake kunshe da lamuran rayuwa da al'adu da suka shafi mutane kuma shi ne ma ya sa UNESCO ta ga muhimmancin ware wannan rana." in ji Dr Chamo.

Harshen Hausa

A cewar Dr Chamo, ana samun ci gaba sosai a Hausa ta yadda aka samu bazuwar harshen da yadda ake amfani da shi a matakai daban-daban.

"Babbar matsalar da ake fuskanta ita ce rashin kaddamar da dokar yin amfani da shi a matakin karatu daga makarantar firamare zuwa sakandare

"Amma idan aka duba duk wasu abubuwa da suke nuna cewa harshe yana ci gaba, za ka ga harshen Hausa ba shi da wata matsala domin iyaye suna koyar da 'ya'yansu," in ji Dr Chamo.

Ya kara da cewa Hausawa suna amfani da harshen a matsayin abin sadarwa kuma ana koyar da shi da nazarinsa a jami'oin kasashen waje da na Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images

"Ana amfani da shi a kotuna da kafafen yada labarai na kasashen waje da na Najeriya."

"Sannan wasu masu magana da wasu harsunan sun saki harsunansu sun koma amfani da Hausa."

A ganinsa, "kusan za a iya cewa arewacin Najeriya kamar shi ne kafar sadarwa da ya hada masu magana da mabanbanta harsuna musamman a jiha irin Filato da Taraba da wasu yankuna na Kaduna."

Ya ce harshen Hausa yana samun ci gaba amma kalubalen da yake fuskanta shi ne rashin samun gudummawar gwamnati.

"Abin takaici ne cewa gwamnatocinmu ba sa mayar da hankali wajen ganin wannan harshe ya ci gaba."

"Amma yanzu Cibiyar Nazarin Harsuna da Fasaha da Fassara a Jami'ar Bayero ta yunkura domin samar da litattafai na kimiyya a cikin harshen Hausa wanda nan ba da jimawa ba ne za a kaddamar da shi domin amfani a makarantun firamare da sakandare", a cewar Dr Chamo.

Kalubalen Harshen Hausa

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A cewar Dr Chamo, babbar matsalar da Harshen Hausa yake fuskanta ita ce ko in kula daga bangaren gwamnati.

"Ba a amfani da shi a matsayin Harshe na kasa, ba a ba da kudade domin gudanar da bincike sannan ba a tabbatar da dokoki da tsarin mulki ya bayar na cewa a yi amfani da harhen uwa a matsayin matakin karatu na firamare da kananan sakandare." kamar yadda ya ce.

"A jihohinmu na arewa wuraren da ake amfani da Hausa, wasu na ganin abin tinkaho ne a ce ba a amfani da harshen Hausa a makarantu

"Wannan ba karamin koma baya ba ne kuma ba karamin sakaci ba ne ga hukuma saboda ta hanyar amfani da wannan harshe ne za a bunkasa shi kuma daliban su samu ci gaba da fahimtar abin da ake koya musu."

"Misali a Netherland, duk duniya ba bu wanda ya kai su iya harshen Ingilishi idan aka dauke kasashen da harshen yake a matsayin harshen uwa, amma ba sa fara amfani da Ingilishi a matsayin harshe da ake koyarwa a makarantu har sai an je sakandare." in ji Dr Chamo.

Ya ce akwai bukatar hukumomi su ba da gudummawa wajen samar da dokokin da suka ba da damar amfani da harshen uwa sannan su taimaka wajen samar da kalmomi da za syi amfani da su a bangare daban-daban na ilimi a yi amfani da shi wajen koyar da Harshen Hausa.

Ya ce yin hakan zai taimaka harshen Hausa ya samu ci gaba da matsayin da ake bukata.

Barazanar gushewar Harsuna

Bayanai na cewa akwai kashi 43 na kimanin harsuna 6,000 a duniya da ke cikin hadarin gushewa sannan harsuna kadan ne ake amfani da su wajen koyarwa a makarantu.

A duniya kuma, kashi 40 na al'umma ba su da damar samun ilimi a harshen da suke ji ko suke ganewa.

A cewar masanin, akwai dalilai da ke jefa wasu harsunan cikin hadari:

1. Masu amfani da harshe suna boyewa ko jin kunya

2. Iyaye ba sa koya wa 'ya'yansu a matsayin makami na sadarwa

3. Kallon iya harsunan da suka karbu a duniya a matsayin birgewa

Ya ce "muddin iyaye ba za su koya wa 'ya'yansu ba kuma ba za a yi amfani da shi a kafafen sadarwa ba kuma gwamnati ba za ta ba shi taimako na kudi don samar da rubuce-rubuce da sauran ayyuka kamar samar da hanyar rubutu, toh hakika harshe zai gushe."

Sai dai a wasu lokutan harsuna suna fuskantar kalubale ta yadda matasa da ba sa jin harshensu na gado. Amma Dr Chamo ya ce abin ba haka yake ba ga harshen Hausa.

"A harshen Hausa, zai yi wahala a je gidan bahaushe a ji yana Turanci da iyalinsa duk zurfin karatunsa sai kalilan da ba a rasa ba." inji sa.

Ya ce idan har irin hakan ba yawa ya yi ba, ba zai zamo matsala ba saboda Hausawa sun rike harshensu suna amfani da shi a duk inda suka je.

A cewarsa, "ko da a kasar waje ka samu Hausawa ba za ka ga suna amfani da Ingilishi ko wani harshe ba, wannan dai harshensu na Hausa shi suke amfani da shi,"

"Kuma a gidaje yara suna tasowa da shi suna ji ana amfani da shi a harkokin yau da gobe, a kafafen yada labarai har da kafar sadarwa ta zamani ita ma tana taimakawa - harshen ba ya samun nakasu." kamar yadda masanin ya fada.

Kiraye-kirayen koyarwa da harshen uwa

Dr Chamo ya bayyana cewa wadannan kiraye-kiraye suna da tasiri sosai musamman manyan harsunan Najeriya uku.

Ya ce jihar Legas ta yi dokar tilasta harshen Yoruba a manyan makarantu saboda a cewarsa "duk wanda yake karatu a manyan makarantunsu, dole sai ya dauki harshen Yoruba a matsayin darasi kafin ya fita."

"Idan har gwamnati ta ba da tallafi aka ba da taimako, wannan zai kara ingancin harsuna kuma yara za su taso sun iya harsunan, za a samu ci gaba." inji Dr Chamo.

Ya ce akwai bambanci tsakanin ilimi da harshe saboda koyarwa da harshen uwa a cewar masanin zai samu sauki wajen iya abu da gane shi, "ba wai sai ka je ka iya harshe kuma ka zo ka yi fassara ba."

Dr Chamo ya ce koyarwa da wasu harsunan na daya daga cikin abubuwan da suke haifar da koma baya saboda "idan da harsunan asali za a koyar toh yanayin da za a samu na ci gaba da kokarin dalibai zai fi haka."

Ya bayyana cewa "duk kasashen da suka ci gaba da harshensu suke amfani wajen gudanar da harkokinsu na ilimi da mulki kamar China da Japan da Jamus da Birtaniya da Italiya ba sa amfani da wani harshe wajen gudanar da harkokinsu na rayuwa da ci gabansu."

Ya ce kiraye-kirayen da ake abu ne mai muhimmanci kuma zai taimaka wajen kawo ci gaba da habaka da bunkasar harsunan gida yadda za su samu matsayi da daukaka a ko ina.

Hanyoyin habaka harshen Hausa

Shi kuwa Dr Muhammad Suleiman Abudullahi, ya ce akwai abubuwa da dama da idan aka mayar da hankali a kai, za a samu habakar harshen:

Yin magana da Harshen:

Malamin ya ce yin magana da harshen asali a koda yaushe zai sa ya kafu sannan a tabbtar da shi a matsayin harshe.

"Ya ce babu abin birgewa mutum ya rika jin cewa wani harshen ya fi nasa. Harshen Hausa ya karbu kuma ya fadada a duniya." inji sa.

Koyar da harshen:

"Jami'oi da yawa a kasashen waje da Najeriya suna koyar da harshen Hausa kuma kara inganta wannan hanyar koyarwar na daya daga cikin hanyoyin da za a kafe harshen." in ji Dr Sulaiman.

Kimanta harshen da daraja shi:

Masanin ya ce samar da abubuwa na ilimi a cikin Harshen zai kara masa kima.

"Fassara na daya daga cikin abubuwan da za su kara inganta harshen da shigo da wasu abubuwa baki da suka shafi ilimi da fadadar karatu, ya kasance da Harshen Hausa." a cewarsa.

Farfado da harkar rubuce-rubuce:

A cewar Dr Sulaiman "Ko da a kafafen sadarwa, ya kamata al'ummar Hausawa su rika amfani da abin da ya shafi bangaren Hausa."

"Domin wannan zai kara kafe Hausa a cikin kundin alakarsu da harshen baki daya."

Tallafi daga gwamnati:

Masanin ya ce kamata ya yi mutane su fara bada tasu gudummawar kafin gwamnati ta shigo cikin lamarin.

"Gwamnati sai ka fara inganta abinka sannan za ta taimake ka, idan al'umma suka yi ita ma gwamnati sai ta kara shigowa don ganin harsunan Najeriya an kara inganta koyar da su tun daga makarantun firamare da sakandare da makarantun gaba da sakandare." in ji Dr Sulaiman.